An Yi Jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
[ad_1]
Da misalin ƙarfe 4:30 na yamma aka gudanar da sallar jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a filin Idi da ke Bauchi.
Dubban jama’a ne suka halarci jana’izar ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Sauran sun haɗa da gwamnoni, ministoci, Sanatoci, malamai, sarakuna daga sassa daban-daban na Nijeriya.
An tsara gudanar da sallar da misalin ƙarfe 3 na rana.
Amma saboda yawan jama’a da cunkoso ba a samu damar gudanar da sallar a kan lokacin da aka tsara ba.
Cikakken bayani yana tafe…
[ad_2]
Source link