Sallar Bana: Yadda Al’umma Ke Bukukuwa Cikin Firgicin ‘Yan Ta’adda Da Tsadar Rayuwa A Arewa

[ad_1]

Al’ummar yankin Arewacin Nijeriya sun gudanar da bukukuwan Karamar Sallah a bana a cikin yanayi mai cike da kalubale, sakamakon tsananin tsadar rayuwa, firgicin ‘yan ta’adda da kuma fargabar hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi jama’a tare da hana masu bacci da idanu biyu.

Duk da farin cikin da jama’a ke yi a yayin bukukuwan Sallah a kowace shekara, a wannan shekarar 2026, shagulgulan sun gudana ne cikin yanayi na kunci da takura ta yadda  iyalai da dama suka gudanar da sallah a cikin matsi kamar yadda wasu yankuna suka dakatar da wasu al’adu bisa ga tabarbarewar sha’anin tsaro.

A lokacin da watan Ramadan na wannan shekarar ya fara a watan Fabrairu, shugabannin addini sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi taimakon ubangiji dangane da kalubalen tattalin arziki da tsaro da ke addabar kasar nan.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na azumi wajen yin addu’o’i domin samun sauki daga matsalolin da kasa ke fuskanta, tare da rokon zaman lafiya ya wanzu a fadin kasar.

Sako na nuni da yadda al’ummar Nijeriya da dama ke tunkarar bukukuwan Sallah a cikin yanayi na tsadar rayuwa, talauci da kuma rashin tsaro da ya ta’azzara a Arewa Maso- Gabas, Arewa Maso- Yamma da Arewa ta Tsakya.

Haka kuma, kungiyoyin kwadago sun bayyana yadda matsin tattalin arziki ke kara tsananta da hana masu walwala kamar yadda kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya da aka fi sani da SSANU ta koka.

Kungiyar ta nuna damuwa  kan yadda jinkirin biyan albashi ke kara tsananta wahalhalun ma’aikata a lokacin azumi. A cewar kungiyar, dubban ma’aikatan jami’o’i da iyalansu na fuskantar matsin kudi a daidai lokacin da da dama ke gudanar da ibadar azumin Ramadan mai alfarma.

Wadannan matsaloli sun shafi yadda mutane da dama a Arewa zuwa Kudu suka gudanar da bukukuwan Sallah a karshen Ramadan, inda da dama suka yi bukin cikin sauki ba kamar yadda suka saba ba.

A jihohin Kano, Katsina,, Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kaduna, da Yobe, jama’a sun fito cikin natsuwa domin gudanar da ibada tare da rokon Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Sai dai wasu daga cikin mazauna yankin Arewa sun bayyana cewa duk da farin cikin gudanar da Sallah karama, zukatansu na cike da damuwa saboda matsalolin da suka dabaibaye su.

Daya daga cikin manyan kalubalen da al’umma suka fuskanta a wannan Sallah shi ne tsadar rayuwa. Rahotanni daga kasuwanni daban-daban a jihohin Arewa sun nuna yadda farashin kayayyaki ya yi sama kafin Sallah kamar kuma yadda teloli suka ci karen su ba babbaka.

Hare- haren ‘yan ta’adda, tashin gwauron zabin man fetur, hauhawar farashin kudin mota daga wannan garin zuwa wancan da rashin tsayayyar wutar lantarki sun haifar da illa sosai wajen hanawa bukukuwan Sallah armashi.

Kayan abinci kamar shinkafa, mai, nama, kayan miya da kayan marmari sun yi tsada sosai, abin da ya sa iyalai da dama suka kasa shirya liyafa ko hidimar Sallah kamar yadda suka saba a baya.

A kasuwannin dabbobi kuwa, farashin dabbobi musamman shanu da ake yin watanda ya karu matuka saboda tsadar sufuri da kuma karancin dabbobin da ake kawowa daga wuraren kiyo. Haka ma farashin kaji ya yi tashin gwauron zabi sama sosai lamarin da ya sa iyalai da dama suka hakura da yanka yadda suka saba.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar yadda tufafi suka yi tsada sosai iyalai da dama sun hakura da dinka sababbin tufafi a yayin da wasu suka kasa dinka tufafin yadda suka saba saboda hauhawar farashin tufafin da na kudin dinki.

Garba Dan Tani ya bayyanawa wakilin mu cewar tsadar tufafi da kayan masarufi sun sa ya kasa sayen sabbin kaya ga ‘ya’yansa kamar yadda ya saba a lokutan Sallah.

Wata uwa mai suna Hajiya Amina Modi ta ce duk da cewa ta yi kokarin ganin ‘ya’yanta sun kasance cikin farin cikin a yayin Sallah, amma ta yi hakan ne a yanayin takaitawa a abin da ta kira ba yabo ba fallasa.

A baya, lokacin Sallah kan kasance lokaci na ziyartar ‘yan uwa da abokai a garuruwa da kauyuka daban-daban amma a yanzu, wasu iyalai sun zabi yin Sallah a gidajensu saboda tsoron hare-hare a hanyoyi ko kauyuka.

Wani mazaunin jihar Zamfara ya ce matsalar tsaro ta sa mutane da yawa sun rage zirga-zirga. “Mutane suna tsoron tafiya saboda matsalar tsaro. A wasu hanyoyi a na jin labarin hare-hare ko satar mutane, don haka mutane sun fi son su zauna a wuraren da suke ganin sun fi samun aminci.”

Duk da wadannan matsaloli, al’umma da dama sun bayyana cewa Sallah har yanzu lokaci ne na ibada, addu’a da karfafa zumunci. Wasu magidanta sun bayyana cewa duk da tsadar rayuwa, sun yi kokarin faranta ran iyalansu da kananan abubuwa domin su ji dadin wannan rana.

A yayin da ake daf da Sallah a cikin wata mai tsalki sababbin hare- haren ta’addanci na kunar bakin wake sun tayar da hankalin al’umma a Borno da ke Arewa Maso- Gabas a inda rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 28 da mutane 108 da suka jikkata.

Yadda ‘yan ta’adda a yankin Arewa suka zafafa ayyukan ta’addanci a cikin watan Ramadan ya kara tsorata jama’a da sanya shakku kan yadda gwamnati da hukumomin tsaro ke fuskantar kalubalen tsaro a kasar nan

Mummunan harin ya faru ne a lokaci daya a ranar Litinin bayan buda- baki a wurare daban- daban da suka hada da babbar kasuwar Litinin da aka fi sani da “Monday Market” da ofishin aika sakonni na gidan waya da kuma a bakin asibitin koyarwa ta jami’ar Maiduguri.

Hare- haren mayakan na Boko- Haram sun faru ne bayan da mayakan suka kai wasu munanan hare- hare a sansanonin sojoji da ke Ajari da Baga da kuma Damboa duka a jihar Borno a yayin da sojojin Nijeriya ke kara sabunta ayyukan yakar ‘yan ta’addan.

Wani mazauni garin, Modu Bukar, wanda ya ga harin da idon sa ya bayyanawa kafafen yada labarai cewar suna zaune kawai suka ji karar fashewa suka kuma fara gudun tsira da rai.

Haka ma daya daga cikin wadanda harin ya faru a kusa da wajen sa suka yi buda- baki ya bayyanawa manema labarai cewar bayan shan ruwa ne sai kwastam suka ji kara sosai a yayin da wasu mutane ke gudun fanfalaki a cikin jini a yayin da ya ce sun ga mutane da dama ba adadi a cikin jini.

LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewar mayakan ISWAP sun kashe kwamandojin soja har guda uku a cikin sati daya a bisa ga munanan hare- haren da mayakan ‘yan ta’addan suka kai masu. Rahotanni sun nuna cewar, a yanzu adadin manyan kwamandojin soji bakwai ne suka mutu a sababbin asarar rayukan wadanda suka hada da Birgediya Janar daya da aka kashe watanni uku da suka gabata.

A watannin baya dai sojoji sun tsananta zazzafan farmaki a wuraren ‘yan bindigar masu hadari da suka hada da dajin Sambisa, Timbuktu, Tuddan Mandara da kuma yankin tafkin Chadi. Sai dai rundunar sojoji ta bayyana cewar ta kashe daruruwan kwamandojin ‘yan ta’addan a yayin da ta matsa lamba wajen fatattakar su.

Kafafen yada labarai sun bayyana cewar mafi yawan mace- macen sun faru ne a sansanonin sojoji da kuma hare- haren kwanton bauna da hatsabiban mayakan ke kaiwa sojojin da ke fafatukar kakkabe ayyukan ta’addanci a yankin.

A bisa ga hare- haren Shugaban Nijeriya, Bola Ahmad Tinubu ya umurci manyan hafsoshin hukumomin tsaro da su koma birnin Maiduguri da zama domin fuskantar ayyukan mayakan gadan- gadan- ba tare da kakkautawa ba.

Tinubu wanda ya yi Allah- wadai da lamarin a jawabin da ya sanyawa hannu a ranar Talata ya bayyana cewar gwamnatinsa ba za ta zuba idanu ta na kallon ‘yan ta’adda na cin karen su ba babbaka ba.

Ya jaddada cewa hare-haren suna nuna alamun rashin karfi da kuma matsananciyar damuwa a tsakanin kungiyoyin ta’addancin, yana mai cewa ci- gaba da hare-haren sojoji ya raunana su matuka.

A yayin tofa albarkacin bakinsa, jagoran ‘yan adawa a Nijeriya, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana alihini a kan sake ta’azzarar ayyukan ta’addanci a Borno tare da cewar ‘yan Najeriya ba su gamsuwa da kalaman Allah-wadai da gwamnati kan yi bayan an kai hari; abin da suke nema shi ne sakamako, domin sakamako ya fi duk wata magana karfi.

Ya ce karuwar kashe-kashen sojoji da fararen hula da dan ta’adda ke yi yana dawo da yanayin abubuwan kunci da suka faru a shekarar 2014, lokacin da ayyukan Boko Haram suka fi kamari a Arewa- Maso- Gabas

Atiku ya bayyana cewar a bayyane yake gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali wajen murkushe ’yan adawa maimakon bayar da kulawar musamman domin magance matsalar tsaro da ke ci-gaba da tsananta. A cewarsa duk da umarnin da aka bayar na murkushe ‘yan ta’addan har yanzu mayakan na ci-gaba da cin karen su ba babbaka.

A bayyane yake cewa matsalar tsaro ta kara jefa al’umma cikin firgici, musamman bayan wasu sabbin hare-haren ta’addanci da suka faru a ‘yan watannin nan. A farkon shekarar nan, wasu ‘yan ta’adda sun kai munanan hare-hare a wasu kauyuka na jihar Kwara, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

Rahotanni sun nuna cewa daruruwan ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan kauyukan, inda suka kona gidaje tare da sace mutane da dama lamarin da ya sanya tsoro da zullimi ga mazauna yankin.

Haka ma a karshen mako, kwana daya gabanin harin ta’addancin a Maiduguri sabbin hare-haren da ake dangantawa da mayakan Bello Turji sun yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu tare da tilastawa mazauna garin Bargaja da ke karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato tserewa daga gidajensu.

Wasu mazauna yankin da suka yi magana kan lamarin sun ce harin wanda ya faru a karshen mako, ya jefa al’umma cikin firgici, inda iyalai da dama musamman mata da yara suka nemi mafaka a wasu wuraren.

A kodayaushe masu sharhi kan al’amuran tsaro kan bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen magance matsalar tsaro a yankin Arewa, sai dai har yanzu lamarin na ci-gaba da ta’azzara.

A ra’ayin mabambantan jama’a, idan aka samu ingantaccen tsaro, manoma da makiyaya za su iya komawa gonakinsu da wuraren kiwo, wanda hakan zai taimaka wajen kara samar da abinci da rage tsadar kayayyaki

Al’ummar yankin Arewa dai na ci- gaba da fatan ganin an samu zaman lafiya da saukin rayuwa domin bukukuwan Sallah su dawo cikin walwala da annashuwa kamar yadda aka saba a baya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *