DSS ta kama wanda ya kitsa harin coci a Kogi a 2025

[ad_1]



Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), sun kama Shafiu Usman, wanda ake zargi da kitsa harin da ya yi sanadin asarar rayuka a cocin ECWA da ke yankin Ayetoro, a Jihar Kogi.

Rahotanni sun ce an kama Usman ne a wata maɓoyarsa a Jihar Gombe, inda yake zaune tare da wasu mambobin ƙungiyarsa bayan sun kai hare-hare a jihohin Neja, Kwara, Kogi da Zamfara.

Aminiya ta ruwaito, yadda aka kashe masu ibada 30 waɗanda yawancinsu yara da tsofaffi ne a ranar 14 ga watan Disamban 2025.

’Yan bindigar sun kai harin ne a kan babura garin Ayetoro-Kiri da ke Ƙaramar Hukumar ‘Kabba/Bunu.

Maharan sun shiga gidaje da coci-coci kafin su tsere zuwa daji.

Wani babban jami’in tsaro ya ce a ranar Juma’a Usman ya amsa cewa shi ne ya kitsa harin cocin, da kuma wasu sace-sace a jihohin Neja, Kwara da Jihar Kogi.

Jami’in ya ƙara da cewa Usman ya bayyana cewa ya yi aiki tare da Ibrahim Dange Battijo, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ke aiki a jihohi da dama, wajen kai harin.

An kuma ruwaito cewa Usman ya amsa laifin aikata satar mutane, fashi da kuma satar shanu, inda ya ce Battijo ne ke ba shi makamai da alburusai.

Bayan harin Kogi, Usman ya tsere zuwa Gombe, amma jami’an DSS sun bi sabunsa tare da kama shi.

Jami’in ya ce wannan kamun ya nuna ƙoƙarin da DSS ke yi na yaƙar ’yan bindiga da ta’addanci, ciki har da ayyukan baya-bayan nan da suka tarwatsa hanyoyin safarar makamai, tare da ceto waɗanda aka sace.

Ana tsare da wanda ake zargin a hannun DSS kuma ana jiran gurfanar da shi a kotu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *