Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ceton Dukkan Ɗalibai 230 Da Aka Sace A Neja
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da nasarar ceto sauran ɗalibai da ma’aikatan makaranta 130 da aka sace daga Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a jihar Neja, lamarin da ya kawo adadin waɗanda aka ceto gaba ɗaya zuwa 230 tare da kawo ƙarshen wannan mawuyacin hali.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a daren Lahadi a Abuja, inda ya ce sakin rukuni na ƙarshe na waɗanda aka sace ya kawo farin ciki ga ƙasa baki ɗaya, musamman ga iyalan da abin ya shafa.
“A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya na tabbatar da cewa dukkan ɗaliban Makarantar Katolika ta Papiri da aka sace, su 230, an kuɓutar da su. Babu ɗalibi ko ɗaya da ya rage a hannun masu garkuwa,” in ji ministan.
Ministan ya ƙara da cewa daliban 130 da aka ceto kwanan nan an miƙa su ga Gwamnatin Jihar Neja domin a haɗa su da iyalansu. Ya yaba da jajircewa da ƙoƙarin jami’an tsaro, yana mai cewa wannan nasara ta ƙara nuna aniyar gwamnati wajen kare rayukan jama’a, musamman yara masu rauni.
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya na matuƙar tausayawa iyaye da masu kula da daliban bisa raɗaɗin da sace-sacen ya jefa su a ciki, tare da musu fatan alheri yayin da suke haɗuwa da ƴaƴansu. Ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa tsaro da kare makarantu a faɗin ƙasar domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari.
[ad_2]
Source link