NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban Jam’iyya na ƙasa
Jam’iyyar NNPP ta sake zaɓen shugabanta na ƙasa, Ajuji Ahmed, tare da sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), a taron gangamin ƙasa da aka gudanar a Abuja a ƙarshen mako.
Ahmed ya dawo kan kujerarsa ba tare da hamayya ba, ta hanyar ƙuri’ar murya a wurin taron, wanda jami’an Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) suka halarta domin sa ido.
Haka kuma, an sake zaben Sakataren Jam’iyya na kasa, Dipo Olayoku, da sauran shugabannin jam’iyya na kasa, dukkansu ba tare da hamayya ba.
A jawabin karɓar zabe, Ahmed ya yi alkawarin cewa sabuwar shugabancin zai ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa jam’iyyar da kuma shirya ta domin samun nasara a zaben 2027.
Ya bukaci mambobin NWC da su dauki sake zabensu a matsayin sabon amanar da za su yi aiki da gaskiya, ladabi da kuma jajircewa wajen kare manufofin jam’iyya.
Ahmed ya ce nasarorin da gwamnatin NNPP ta samu a Jihar Kano na nuna irin abin da ‘yan Najeriya za su iya tsammani idan jam’iyyar ta karɓi mulki a matakin tarayya a 2027.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana taron a matsayin muhimmin mataki wajen bunkasa jam’iyyar da tsara makomarta.
Ya shawarci shugabancin jam’iyyar da su inganta haɗin kai, adalci da kuma shigar da kowa, tare da jaddada cewa babu wani bangare na jam’iyyar da ya kamata ya ji an ware shi.