NYCN Ta Yi Allah-wadai Da Harin Bam A Maiduguri, Ta Buƙaci Ƙarfafa Matakan Tsaro
Ƙungiyar Matasa ta Ƙasa (NYCN), ta yi Allah-wadai da hare-haren bam da suka afku a birnin Maiduguri na Jihar Borno, waɗanda suka yi sanadin asarar rayuka da lalata dukiyoyin al’umma da dama.
Ƙungiyar ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, tana mai jaddada cewa bai kamata wani ɗan ƙasa ya rayu cikin fargaba a cikin al’ummarsa ba.
- Mutum Ɗaya Ya Mutu A Faɗan Daba A Jihar Kano
- Sojoji Sun Ƙwato Shanun Sata A Filato
Ta yaba da gaggawar tura jami’an tsaro, tare da kira na a ɗauki matakai masu ɗorewa domin kiyaye sake afkuwar makamantan harin, ciki har da inganta tattara bayanan sirri da tsaron al’umma.
NYCN ta kuma buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi tare da ɗaukar matakai masu tsauri da haɗin gwuiwa domin magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar nan.
Haka kuma ta roƙi matasa da su kasance masu natsuwa da sanya ido, da kuma mara wa hukumomin tsaro baya, tare da jaddada aniyarta na bunƙasa zaman lafiya da ci gaban ƙasa.