Makiyaya sun kashe manomi a gonarsa a Borno




Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki a wata gonar wake, inda suka kashe wani mai gonar yana tsaka da aiki a Ƙaramar Hukumar Monguno da ke Jihar Borno.

Shaidu sun ce makiyaya kimanin 10 ne  suka kai harin bayan sun kutsa da shanunsu suka yi kiwo a wasu gonaki da misalin ƙarfe 12:20 na  ranar Asarar a Dajin Ngolom.

Ɗaya daga cikin manoman da makiyayan suka kutsa gonarsu, Abatcha Abatcha da ke yankin Gana Ali Ward, manoman sun buƙaci makiyayan su bar gonakin, amma sai lamarin ya rikice zuwa tashin hankali.

“Makiyaya sun kai mana hari da sanduna. Ɗaya daga cikin manoman da Allah Ya yi wa rasuwa, Bakulu Bafindi mai shekaru 30 daga unguwar Sabon Lamba a Maiduguri, ya samu munanan raunuka sakamakon arangamar, inda aka garzaya da shi Babban Asibitin Monguno, daga bisani wani jami’in lafiya ya tabbatar da rasuwarsa.”

Tuni dai aka ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawarwaki na asibitin kafin daga bisani a miƙa ta ga ’yan uwansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Nahum Daso ya bayyana cewar, tuni jami’an tsaro da ’yan banga na yankin suka ƙaddamar da farautar maharan, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a tsakanin manoman.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *