Yadda Ake Soya Doya Da Kifi Da Kwai
[ad_1]
Assalamu Alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake soya Doya da Kifi da Kwai:
Abubuwan da ake bukata:
Doya, Kifi tayitus, Kwai, Tattasai, Attaruhu, Albasa, Magi, Gishiri, Kori, Mai.
Ga kuma Yadda ake hadawa:
Da farko za a fere Doya a yayyanka ta sannan a wanke ta, sai a dafa ta, bayan ta dahu sai a kwashe ta a daka ta kamar yadda ake ‘Yam bolls’ a ajiye a gefe.
Sannan a daka ko a yayyanka Tattasai da attaruhu, sai a yanka Albasa, sai a kawo abin suya a dora shi a wuta a zuba Mai kadan sai a zuba Albasa tare da dakakken Tattasai da Taruhu a soya su sama-sama, sannan a kawo Magi, Gishiri, Kori a zuba daidai yadda zai isa.
Sannan a kawo Kifi wanda dama an yi ganishin dinsa an soya shi, an cire masa kaya an faffasashi an gaureya shi sosai sannan an cakuda shi, sai a sanya a kilashi sannan a ajiye a gefe.
Sai a dakko Doyar da a daka, azuba soyayyen kayan a ciki, a gaureya sosai ya kama jikinsa. Sai a fara diba a hannuayi yadda ake dunkula Doya sai a dan buda tsakiya sannan a dakko wannan Kifin da aka dunkulashi guda daya a sa a tsakiya, sannan sai a rufe a sake dunkule shi bayan an rufe ya zama boll, haka za a yi wa ko wanne har a gama.
Sai a dora mai a wuta a sa Albasa idan ya yi zafi a fara soyawa. Ana ci da jajjagen miya ko da yaji. A ci dadi lafiya.
[ad_2]
Source link