Barayin Shanu Sun Kashe DPO A Karamar Hukumar Rimi Ta Jihar Katsina

[ad_1]

‘Yan bindiga sun kashe DPO mai kula da karamar hukumar Rimi ta Jihar Katsina, CSP Muhammad Sani Kabir a lokacin fatattakar wasu da ake zargin Barayin shanu ne.

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta Jihar Katsina ta tabbatar da cewa an kashe wasu da ake zargin Barayin ne lokacin aikin hadin gwiwa da ya hada da jami’an tsaro da sauran al’umma.

  • Tsarin Siyasar Kano: Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura…
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 33 A Kebbi

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasir Mu’azu ya bayyana alhininsa game da rasuwar jami’in da aka kashe a lokacin da yake jagorantar samamen.

Sanarwar ta ce an samu rahotanni masu sahihanci cikin dare daga shugabannin al’umma na karamar hukumar Rimi da suka hada da kansila, mambobin jam’iyyar APC da mai garin Karare da ke Rimi game da zuwan mutanen da ake zargin Barayin ne a garin Magaji da ke mazaBar Majen-Gobir.

Bayan samun labarin, DPO din ya tattara jami’an tsaro zuwa yankin. An ba da rahoton cewa, mutanen da ake zargin sun mamaye Majen-Gobir, abin da ya sa mazauna yankin daukar mataki.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru da sanyin safiya, daidai lokacin da ake Sallar Asuba, inda aka kwato mafi yawan shanun da aka sace.

Ya ce yanzu haka jami’an tsaro uku da suka samu raunuka suna karBar kulawa a asibitin koyarwa ta Jihar Katsina, yayin da aka kai gawar DPO zuwa Zariya a Jihar Kaduna domin yi masa jana’iza.

Ma’aikatar ta yaba da bajintar jami’an tsaro da kuma al’umma, tare da nanata kokarin gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, inda ya jaddada kokarinta na kawar da masu aikatar laifuka da kuma tabbatar da tsaro a yankin.

Ma’aikatar ta yi alhini game da rahsin CSP Muhammad Sani Kabir tare da yin addu’ar Allah ya saka masa da Aljannatul Firdaus.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *