Albashin sanatoci 109 zai biya farfesoshi 4,709

[ad_1]



Aminiya ta gano cewa kimanin Naira biliyan 2.354 da ake kashewa a albashi da kuɗin gudanar da ofisoshin sanatoci 109 na Najeriya a kowane wata, ya isa a biya albashin farfesoshi 4,708 a jami’o’in ƙasar.

Tazarar albashi tsakanin masu mukaman siyasa da malamai a jami’a na ci gaba da zama abin muhawara a ƙasar.

A kwanakin baya, kafafen sada zumunta sun cika da hoton Farfesa Nasir Hassan-Wagini daga Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, wanda aka gani yana sayar da kayan lambu a kasuwar Batsari. Shi da wasu malaman jami’a da dama sukan yi wasu sana’o’i domin samun abin rayuwa.

Binciken Aminiya ya nuna cewa ana biyan farfesa matsakaicin albashi na ₦500,000 a wata, a yayin da sanata ke karɓar Naira miliyan 21.6 a wata.

A ranar 14 ga Agusta, 2024, Sanatan Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila ya shaida wa BBC Hausa cewa yana karbar albashin Naira miliyan 21.6 l a wata.

Ya ce, “Farfesoshi na karbar fiye da Naira miliyan 1. Idan an cire haraji da wasu kuɗaɗe, sai ya dawo Naira dubu ɗari shida. Amma kowanne sanata yana karbar Naira miliyan 21 a wata don gudanar da ofis,” in ɗan Majalisar Dattawan.

Bayanin nasa ya zo ne bayan Hukumar Tsara Albashi ta Ƙasa (RMAFC) ta ce sanatoci na karbar Naira miliyan 1.06 a wata a matsayin albashi da alawus.

Shugaban Hadaɗɗiyar Ƙungiyar Malaman Jami’a (CONUA), Dakta Niyi Sunmonu, ya ce malamai sun kasance a kan tsarin albashi ɗaya tun 2009, sai bara da gwamnati ta ƙara albashi da kashi 35% ga farfesoshi da kuma 25% ga sauran malamai.

Dakta Niyi Sumonu ya ce, “Albashin gaba ɗaya kimanin Naira dubu ɗari bakwai ne, amma bayan haraji da sauran cire-cire, sai ya koma ₦500,000.”

Ya ƙara da cewa farfesoshi ba za su iya samun rancen Naira miliyan goma zuwa miliyan 15 ba don sayen mota, duk da tsarin biyan bashin da ƙungiyoyin haɗin gwiwa da adashin fata ke bayarwa.

Ya bayyana cewa a shekarun 1960, farfesoshi su ne na uku girman albashi a Najeriya bayan Firayim Minista da Alƙalan Kotun Koli, sa’annan suna karɓar kuɗin gudanar da ofis da ’yan aiki.

“A yau, albashi ya tsaya cak fiye da shekara 16. Wasu malamai ba sa iya zuwa ofis kullum saboda rashin kuɗin sufuri. Wasu sau ɗaya suke zuwa a mako. Ba sa iya ƙarfafa ɗalibai kamar yadda ake yi a da,” in ji shi.

Sunmonu ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa, yana mai gargaɗi cewa jami’o’in Najeriya na fuskantar barazanar rushewa nan da shekaru 5 zuwa 10.

Yadda malaman jami’o’i ke rayuwa

A wata hira da ta bazu a kafafen sada zumunta, Farfesa Balarabe Abdullahi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) Zaria ya ce albashinsa bai isa ya saka ɗansa a makaranta mai inganci a Abuja.

Ya gargaɗi cewa Najeriya na fuskantar barazanar rugujewar fannin ilimi idan ba a gyara tsarin ba.

“Albashinmu ba ya isa. Farfesoshi da ya kamata su zama jagororin ci-gaban ƙasa suna cikin ƙuncin rayuwa. Wasu na kuka saboda ba su da abinci. Wasu na sayar da kayan miya don rayuwa. Muna ta yawo don neman ƙarin kuɗi ta hanyar koyarwa a wasu jami’o’i,” in ji shi.

Farfesa Samuel Agu na Jami’ar Jihar Abia ya ce yana dogaro da koyarwa a wasu jami’o’i da sana’o’i don cike giɓin buƙatu. “Albashina ya taɓa kaiwa ₦460,000, amma bayan haraji sai ya koma ₦390,000. Yanzu ya kusa ₦490,000. Wannan shi ne gaba ɗaya, ba ni da wani alawus,” in ji shi.

Farfesa Chukwudi Ibe, Shugaba Tsangayar Adabi na Jami’ar FUTO ya ƙara da cewa, “Albashinmu ba ya isa. Hauhawar farashi ta cinye shi. Abin tausayi ne. Mu ne hasken al’umma, amma Najeriya ba ta ganin mu haka.”

Yawan aiki na shafar lafiyarmu — Malamai

Malaman jami’an sun bayyana cewa barin ƙasar da abokan aikinsu ke yi domin neman rayuwa mai sauƙi a ƙasashen waje ya sa su ke fama da nauyin aiki mai yawa, wanda ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwarsu da jininsu.

Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce wannan matsala ta ƙara ta’azzara sakamakon tsananin ƙuncin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar, inda malamai da dama ke kamuwa da cututtuka har ma da rasa rayukansu.

A watan Fabrairu 2024, ASUU ta bayyana cewa ta rasa mambobi 46 a yankin Abuja sakamakon matsin tattalin arziki da rashin ingantaccen albashi da yanayin aiki mara kyau. Yankin Abuja ya ƙunshi Jami’ar Abuja; Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna; Jami’ar Tarayya, Lafia; Jami’ar Jihar Nasarawa, da Jami’ar Ibrahim Babangida, Lapai.

“Cikin shekaru goma da suka gabata, malamai da dama sun bar ƙasar domin neman rayuwa mai sauƙi, lamarin da ya bar waɗanda suka rage cikin tsarin suna fama da nauyin aiki mai yawa. Wadanda suka rage suna ƙara dare musu gwiwa a kullum saboda rashin albashi mai kyau da yanayin aiki mara kyau,” in ji Salahu Muhammed, mai kula da yankin Abuja na ASUU.

“Ya kamata a lura cewa ƙungiyar ta rasa mambobi da dama a wannan lokaci sakamakon wahalhalun aiki, damuwa ta ƙwaƙwalwa da ta zuciya, da cututtuka masu alaƙa da waɗannan matsaloli. Misali, jami’o’in da ke yankin Abuja sun rasa mambobi 46.

“A gaskiya, kwana biyu da suka gabata, ƙungiyar ta rasa wani shahararren Farfesa a fannin Kifi, Farfesa Johnson Oyero daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna, sakamakon rashin samun ingantaccen magani,” in ji Salahu.

A kwanakin baya, an ƙaddamar da gidauniya tarl naira miliyan 13 don biya wa Farfesa Abubakar Roko na Sashen Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato (UDUS) kuɗin magani. Duk da gudummawar da aka tara, ciki har da naira miliyan 5 daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Farfesa Roko ya rasu daga bisani.

Tsarin zalunci ne tushen matsalar

Wani masani ɗan Najeriya da ke zaune a Jamus, Dakta Mushin Ibrahim, ya danganta matsalar da malamai ke fuskanta da tsarin rashin adalci, wanda ke ba da ƙarancin muhimmanci ga malamai da fannin ilimi gaba ɗaya.

Ya rubuta a shafinsa na Feshin cewa:  “Ya zama kamar al’ada ce a kafafen sada zumunta mu ci gaba da kuka kan halin da malamai ke ciki a Najeriya. Mun yi irin wannan tattaunawa makonni da suka gabata, bayan labarin ban tausayi na Farfesa Abubakar Roko ya bayyana. Allah Ya gafarta masa, ya kula da iyalansa, amin.

“Yanzu, babu wanda ke musun cewa matsalar tana nan. Wasu na iya cewa farfesoshi su yi wannan ko wancan don samun ƙarin kuɗi fiye da albashinsu. Amma me ya sa ba za su samu albashi mai kyau ba? Ba haka ya kamata a yi da duk wani ma’aikaci ba?”

’Yan siyasa na wadaƙa, malamai na wahala

“’Yan siyasa na cike da kuɗi. Jin daɗinsu da na hadimarsu da sauran masu kusanci da su ba abin magana ba ne. Ba wai kawai suna karɓar albashi mai tsoka ba ne, suna kuma samun alawus da sauransu a yayin da suke kan mulki da ma bayan sun sauka,” in ji wani mai sharhi.

Hassan Soweto, Ƙo’odinetan Ƙasa Kungiyar Kare Haƙƙin Ilimi, Hassan Soweto, ya bayyana cewa ba daidai ba ne a ce ’yan siyasa na karɓar albashi fiye da malaman jami’a, musamman farfesoshi, yana mai cewa hakan ba adalci ba ne, kuma yana aika saƙo mara kyau ga matasa masu sha’awar zama malamai.

Ya ce: “Rashin kyakkyawan albashi da farfesoshi da malamai ke karɓa a jami’o’in Najeriya shi ne abu na farko da kowanne ɗalibi ko wanda ke sha’awar zama malami ke fuskanta.

“Idan mutum ya shiga jami’a ya ga yadda malamansa ke rayuwa cikin ƙunci, hakan yana haifar da tasiri a zuciyarsa. Yana nuna masa yadda rayuwarsa za ta kasance idan ya zaɓi zama malami.

“Saɓanin yadda aka saba gani a zamanin bayan mulkin mallaka ba, albashin malamai a yanzu bai taka kara ya karya ba. Saboda haka ba abin mamaki ba ne cewa a cikin matasa yanzu—wata al’ada da ta zama ruwan dare—ana kallon ilimi a matsayin hanyar faranta ran iyaye, yayin da nasara ke da alaƙa da ‘faɗi-tashi’, ko ta hanyar halal ko ta hanyar da ba ta dace ba.”

Ya ƙara da cewa: “Ba daidai ba ne a ce sanata na karɓar fiye da farfesa. A gaskiya, a duk al’umma da ke son ci gaba da bunƙasa, bai kamata ’yan siyasa su karɓi albashi fiye da malamai ba, balle farfesoshi, domin siyasa ba aiki ba ne. Bai kamata a ɗauke ta a matsayin sana’a ba. Siyasa ya kamata ta zama hidima ta gaskiya da mutum ke yi don al’ummarsa, mazaɓarsa, ko ƙasarsa.”

Soweto ya ce don Najeriya ta sake daidaita burinta na ci gaban ƙasa, “wannan kuskure” dole ne a gyara, yana mai jaddada cewa hakan ne kawai zai dawo da martabar ilimi.

“Lokacin da matasa za su yi alfahari da zuwa makaranta, suna fahimtar cewa ilimi ne hanyar samun nasara. Amma a yanzu ba haka lamarin yake ba, domin siyasa—wadda bai kamata ta zama sana’a ba—ta fi zama mai riba,” in ji shi.

Soweto ya bayyana matsalar a matsayin abin ke hana ci gaban ilimi a Najeriya. Ya ce domin Najeriya ta sake daidaita burinta na ci gaban ƙasa, dole ne a gyara wannan “ba daidai ba,” yana mai jaddada cewa wannan ne kawai hanyar da za a dawo da mutuncin ilimi.

“Lokacin da matasa za su ji daɗin zuwa makaranta, su fahimci cewa ilimi shi ne hanyar samun nasara. Amma a halin yanzu, ba haka lamarin yake ba, domin wasu abubuwa kamar siyasa — wanda bai kamata ya zama sana’a ba — sun fi samun riba,” in ji shi.

Albashin malaman jami’a a sauran ƙasashen Afirka

Najeriya na ɗaya daga cikin manyan tattalin arziƙin Afirka guda biyar, tare da ƙasashen Afirka ta Kudu da Masar da Morocco da Kenya.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa a Najeriya ne malamai ke samun ƙarancin albashi fiye da sauran ƙasashen.

A cewar SalaryExpert:

– Afirka ta Kudu: Malamin jami’a na samun albashi na shekara R818,907 (N71.4m), tare da bonus na R28,089 (N2.4m). Sabon malami (shekaru 1–3 na ƙwarewa) na samun R578,940 (N50.5m), yayin da babba (shekaru 8 zuwa sama) ke samun R1,025,119 (N89.4m) a shekara.

– Maroko: Malamin jami’a na samun albashi na shekara MAD 300,290 (N50.8m), ban da bonus na MAD 10,300 (N17.4m). Sabon malami na samun MAD 211,288 (N35.7m), yayin da babba ke samun MAD 374,125 (N63.3m) a shekara.

– Kenya: Matsakaicin albashin wata-wata na farfesa a jami’o’in Kenya ana kiyasta shi a KES 241,875 (N2.8m). Mafi ƙaranci na KES 125,866 (N1.4m), yayin da mafi girma ke kai KES 370,866 (N4.3m) a wata.

– Nijar: A cewar World Salaries, matsakaicin albashin shekara-shekara na malamin jami’a shi ne XOF 5,771,600 (N15,747,986). Mafi ƙaranci XOF 2,773,700 (N7,568,124), yayin da mafi girma ke kai XOF 9,060,600 (N24,722,122). Ba a bayyana ko albashin kafin cirar haraji ba ne.

– Kanarin: Farfesa a jami’a na samun matsakaicin albashi na shekara XAF 8,590,400 (N23,602,723). Albashin na iya bambanta daga XAF 4,129,300 (N11,345,539) zuwa XAF 13,441,600 (N36,931,733) a shekara.

– Gambiya: Malami a jami’a na samun albashi kimanin GMD 265,000 (N5,602,622) a shekara. Albashin na iya bambanta daga GMD 143,200 (N3,027,530) zuwa GMD 399,900 (N8,454,674) a shekara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *