Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin tantance ma’aikata sama da 7,000 ta hanyar Intanet domin tabbatar da bayanansu da kuma kawar da ma’aikatan bogi.
Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar (CSC), Hajiya Rabi Shu’aibu Jimeta, wacce ke jagorantar aikin, ta ce wannan shiri na nufin tabbatar da sahihancin bayanan ma’aikata.
Ta bayyana cewa za a kammala aikin cikin makonni takwas, kuma duk ma’aikatan da abin ya shafa za a ɗauki bayanansu domin sauƙaƙa samun bayanai.
Hajiya Jimeta, ta ce an keɓe ma’aikatan shari’a, hukumar malamai (Teachers Service Commission), da ma’aikatan lafiya, saboda hukumominsu na da tsarin tantancewa nasu.
Ta ƙara da cewa aikin na daga cikin shirin gyaran ma’aikata da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin gano ma’aikatan bogi da kuma waɗanda suka wuce lokacin ritaya.
“Bayan kammala aikin, za mu bai wa gwamnati shawara ta ɗauki sabbin ma’aikata da suka cancanta domin maye gurbin giɓin da ake da shi,” in ji ta.
A nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) reshen Gombe, Kwamared Yusuf Ash Bello, ya yaba da matakin.
Ya ce aikin na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da inganta tsarin ma’aikata.
“Muna goyon bayan wannan aiki saboda zai samar da sahihin adadin ma’aikatan gwamnati. Ba za mu ci gaba da dogaro da bayanan bogi ko takardun bogi ba,” in ji Bello.
Wasu daga cikin ma’aikatan da aka riga aka tantance sun nuna farin cikinsu, inda suka bayyana cewa hakan zai taimaka wajen inganta hakkokinsu da ƙarin girma.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link