Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

[ad_1]


A yayin taron sauyin yanayi na MDD na watan Satumba, a karon farko a tarihin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar da sabbin matakan kasa na samar da gudunmawa ga cimma nasarar yarjejeniyar sauyin yanayi ko NDCs a takaice, mai kunshe da dukkanin burikan tattalin arziki masu nasaba da kawo karshen fitar da dukkanin nau’ikan hayaki masu dumama yanayi.

To ko me wadannan matakai suka kunsa? Amsar a bayyane take, domin kuwa Sin ta sha alwashin nan zuwa shekarar 2035, za ta rage fitar da nau’o’in hayaki masu dumama yanayi da kaso 7 zuwa kaso 10 bisa dari, daga kololuwar matakan fitar da su, da kara adadin kasonta cikin jimillar makamashin da take amfani da shi daga hanyoyin da ba na kona mai ko iskar gas ba zuwa sama da kaso 30 bisa dari. Kana Sin din za ta fadada adadin cibiyoyin samar da lantarki ta iska, da hasken rana zuwa sama da rubi shida kan matsayin da take a shekarar 2020.

Baya ga wadannan matakai, shugaban na Sin ya gabatar da shawarwari uku, da suka hada da bukatar karfafa gwiwa domin tunkarar aikin da aka sanya gaba, da kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su sauke nauyin dake wuyansu, da jaddada muhimmancin zurfafa hadin gwiwa. Wanda hakan ya samu matukar karbuwa tsakanin masharhanta, da masu lura da harkokin da suka shafi sauyin yanayi. Duk da haka, akwai wasu sassa musamman na yammacin duniya da suka nuna rashin gamsuwa da kwazon na kasar Sin. Idan wadannan bangarori sun kawar da kai daga shaidu na zahiri, masu nuni ga manyan nasarori da Sin ta cimma a wannan fanni.

Ko shakka babu, yunkurin kasar Sin na cimma nasarar kawar da fitar da hayakin carbon daga kololuwar matsayinsa nan zuwa shekarar 2060 ya cancanci yabo. Kuma abu ne mai yiwuwa, duba da nasarorin baya da kasar ta cimma, ciki har da nasarar da ta samu ta rage fitar da hayakin na carbon a shekarar 2020 da kaso 60 bisa dari kan na shekarar 2005, adadin da ya haura hasashen nasarar da aka yi fata da karin kaso 40 zuwa 45 bisa dari.

A fannin cimma burikan kafa karin cibiyoyin samar da lantarki ta iska da hasken rana kuwa, yanzu haka kasar Sin ta kai inda take buri, tun ma kafin shekarar 2030 da a baya aka tsara cimma burin hakan. A daya bangaren kuma, tana tallafawa wasu kasashe masu tasowa, karkashin manufofi irin su hadin gwiwar gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, wajen aiwatar da dabarun dakile sauyin yanayi, da jure tasirinsa, da aiwatar da dubban matakai masu nasaba da hakan.

Tabbas kowa ya yarda cewa shawo kan kalubalen sauyin yanayi na bukatar hadin gwiwar dukkanin sassa, kuma la’akari da gudunmawar da Sin ke bayarwa a gida da waje, ma iya cewa tana kan turbar jagorantar duniya wajen cimma nasarar hakan ta yadda za a gudu tare a tsira tare, wato a kai ga cin gajiyar kyakkyawan muhallin duniya mai kayatarwa. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *