Mutane 25 sun mutu, 14 sun nutse a hatsarin jirgin ruwa a Yobe
[ad_1]
Hatsarin kwalekwale ya yi ajalin aƙalla mutum 25, yayin da aka ceto 13, sannan wasu 14 suka ɓace a Ƙaramar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:48 na yamma a ranar Asabar, lokacin da wani kwalekwale ɗauke da fasinjoji 52 ya kife a kan hanya daga garin Adiyani da ke ƙaramar hukumar Guri ta Jihar Jigawa zuwa garin Garbi a Ƙaramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe.
An bayyana cewa mutanen da hatsarin ya rutsa da su suna dawowa ne daga garin Adiyani inda suka je kamun kifi, noma da sauran harkokin kasuwanci, sai kwale-kwalen ya kife a tsakiyar ruwa.
Ya zuwa yanzu, an yi nasarar ceto fasinjoji 13, yayin da ake ci gaba da bincike da aikin ceto domin gano waɗanda suka ɓace da kuma ƙarin gawawwaki. Hukumomin tsaro, masu ba da agajin gaggawa da ’yan sa kai na al’umma na ci gaba da aiki ba tare da gajiyawa ba.
Tun daga lokacin, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tura ƙungiyar bincike da ceto daga Bade da Nguru domin tallafawa tawagar da ke gudanar da aikin.
Hukumomin sun miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da tabbatar da cewa ana yin duk abin da ya dace don tallafawa waɗanda suka tsira da iyalan da abin ya shafa.
A cikin saƙon ta’aziyya, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jajanta wa iyalan da suka rasa ’yan uwansu da kuma al’ummar ƙananan hukumomin Nguru da Guri. Ya kuma ba da umarnin a samar da duk wani tallafin lafiya da kayan aiki ga waɗanda abin ya shafa da ke karɓar magani.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin hanzarta kula da marasa lafiya ba tare da ɓata lokaci ba domin ceton rayuka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link