Zargi: Yadda Amarya Ta Kashe Mijinta Da Gubar Ɓera A Jigawa
[ad_1]
Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta kama wata amarya, da ta yi aure kwanan nan a kauyen Gauza, karamar hukumar Jahun ta jihar kan zargin zuba guba a abincin mijinta, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Lamarin, a cewar wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam Anipr, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 23 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 5:00 na yamma.
- Sirrin Mallakar Miji
- Gyaran Amarya Kafin Lokacin Aure
Ya ce binciken farko ya nuna cewa, marigayin ya ci abincin da matarsa ta girka masa ne a gidansa kafin ya fara rashin lafiyar ba zato ba tsammani.
An garzaya da shi asibiti mafi kusa don neman magani amma nan take yace ga garin ku nan a yayin da likitoci ke kula da lafiyarsa.
Bayan lamarin, jami’an ‘yansanda da ke aiki a babban ofishin ‘yansanda na Jahun sun fara bincike, wanda ya kai ga kama matar a matsayin babbar wacce ake zargi.
A lokacin da ake yi mata tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa laifin zuba maganin ɓera acikin abincin mijinta.
Sai dai ta bayyana cewa, iyayenta ne suka tilasta mata auren, lamarin da ta yi ikirarin cewa, shi ya tunzura ta aikata wannan laifin.
Kwamishinan ‘yansanda ya ba da umarnin a mayar da shari’ar zuwa ga Sashen Binciken Laifuka na Jiha (SCID) da ke Dutse don yin cikakken bincike.
Za a gurfanar da wacce ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.
[ad_2]
Source link