Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket
[ad_1]
Wani haziƙin matashin ɗan wasan Cricket mai shekara 17 ɗan asalin ƙasar Australiya ya mutu a yau Alhamis bayan ƙwallo ta buge shi a lokacin wasa.
Ƙwallon ta bugi, Ben Austin a wuyansa ne duk da cewa yana sanye da hular kariyar kai (Helmet) a lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙwallon da aka bugo.
Nan take aka garzaya da shi asibiti cikin mawuyacin hali, daga bisani rai ya yi halinsa.
“Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar haziƙi Ben ɗinmu, wanda ya mutu da safiyar yau Alhamis,” in ji mahaifinsa Jace Austin a cikin wata sanarwa.
A cewar jaridar ABC News, matashin ɗan wasan bai sanya rigar da ke kare wuyansa ba, hakan ne ya sa ƙwallon ta dufafe shi.
Austin ya kasance ƙwararren mai buga ƙwallo, wanda ƙungiyarsa ta Ferntree Gully Cricket Club ta ɗauke shi a matsayin “ɗan wasan Cricket mai hazaka, babban jagora kuma matashi mai ban mamaki”.
‘Yan wasa daga ƙungiyoyin biyu na India da Australia a ɓangaren mata da ke buga wasan Cricket na duniya sun sanya baƙaƙen kambu domin alhinin mutuwarsa.
Yau dai kimanin shekaru 11 rabon da wani ɗan wasan Cricket ya mutu a lokacin wasa, tun bayan da shahararren ɗan wasan nan ɗan asalin ƙasar Australia Test Phillip Hughes ya mutu a 2014.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link