Matakin Soke Harajin Kwastam Ya Shaida Niyyar Kasar Sin Ta Taimakawa Kasashen Afirka A Kokarinsu Na Zamanantar Da Kansu

[ad_1]

“Yadda kasar Sin ta soke harajin kwastam a kan kayayyakin kasashen Afirka, kyakkyawar dama ce gare mu wajen fitar da kayayyakinmu zuwa gare ta.”

“Hakan na nufin karin damammaki ga kasashen Afirka wajen bunkasa masana’antu da ma samar da karin guraben aikin yi.”

“Hakan zai ba mu fifiko ta fannin farashin kaya, haka kuma zai samar mana da karin kuzari na habaka ayyukan kere-kere da inganta kayayyakinmu……hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, bai tsaya ga samar da gudummawa kamar yadda aka saba ba, a maimakon haka, yana taimaka wa kamfanonin kasashen Afirka samun damar sa hannu cikin ayyukan zamanantar da kasashensu.”

Martani ke nan da bangarori daban daban na kasashen Afirka da suka hada da ’yan siyasa da ’yan kasuwa da masana da sauransu suka mayar, biyowa bayan yadda kasar Sin ta sanar da fara soke harajin kwastam a kan dukkannin kayayyakin da suke shigowa kasar daga kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diplomasiyya da ita, daga ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa.

Dalilin da ya sa suka nuna babban yabo ga wannan matakin da kasar Sin ta dauka, shi ne saboda hakan zai biya bukatun kasashen Afirka na raya kansu, duba da cewa, kasashen Afirka sun dade suna fuskantar matsaloli ta fannin fitar da kayayyakinsu ketare, da ma karancin samun mabambantan ginshikan tattalin arziki. In mun yi nazari a kan Nijeriya, za mu gano cewa, tattalin arzikin kasar yana matukar dogara da fitar da danyen mai zuwa ketare, don haka sauyin farashin mai a duniya ya kan haifar da matsaloli ga harkokin kudi har da rayuwar al’umma a kasar. Don neman shawo kan wannan matsala, gwamnatin kasar ta gabatar da ajandar da ake kira Renewed Hope, a kokarin bunkasa tattalin arzikin kasar daga fannoni daban daban, ta yadda za a kai ga tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arzikin kasar. A game da matakin da kasar Sin ta dauka na soke harajin kwastam a kan kayayyakin kasashen Afirka, jaridar BusinessDay ta Nijeriya a wata makalarta ta bayyana cewa, kasar Sin ita ce abokiyar ciniki mafi girma ga Nijeriya, kuma kudin ciniki a tsakanin kasashen biyu ya dada karuwa da sauri cikin ’yan shekarun baya. Matakin da kasar Sin za ta dauka na soke harajin kwastam zai kasance babbar dama ga Nijeriya wajen kara fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin da ma kyautata tsarinta na ciniki, kuma hakan zai tabbatar da kyakkyawar makoma ga hadin gwiwar kasashen biyu.

Har ila yau, martanin da kasashen Afirka suka mayar sun kuma shaida bukatunsu game da ciniki mai adalci, musamman a yayin da wasu suka mai da hannun agogo baya a kokarin da ake yi na tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya waje daya da yaki da kariyar ciniki. A yayin da wasu kasashe suke ta da “yakin haraji” a duniya, ga shi kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen Afirka, wanda hakan ya shaida ma’anar abokantaka. A kwanan baya, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres shi ma ya yaba da matakin da kasar Sin ta dauka, inda kuma ya yi kira ga kasashe masu ci gaba da masu karfin tattalin arziki da su dauki irin wannan mataki.

A shekarar 2005, kasar Sin ta soke harajin kwastam a kan wasu kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Afirka da suka fi fama da koma bayan tattalin arziki. Ga shi yanzu, har ta kai ga soke harajin kwastam a kan dukkanin kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diplomasiyya da ita. Hakan ya nuna cewa kasar Sin na kara bude kofarta ga kasashen Afirka.

A bana ake cika shekaru 70 da kasar Sin ta fara kulla huldar diplomasiyya da kasashen Afirka. Cikin shekarun 70 da suka wuce, har kullum Sin da kasashen Afirka sun kasance aminan juna. Yadda kasar Sin ta soke harajin kwastam a kan dukkanin kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diplomasiyya da ita, ya sake isar da sako ga duniya, wato kasar Sin abokiyar tafiya ce ga kasashen Afirka a kan hanyar zamanantar da kansu. (Lubabatu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *