Da Ɗumi-ɗumi: Mbappe Ba Zai Buga Wasan Real Madrid Da Benefica Ba

[ad_1]

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Kylian Mbappe ba zai buga wasan zagaye na biyu da kungiyarsa zata buga da SL Benfica ba a gasar zakarun Turai ta bana sakamakon raunin da ya samu a kafarsa ta hagu.

Hakan ya zo kwana daya kafin a buga wasan a filin wasa na Santiago Bernabeau dake birnin Madrid na kasar Sifaniya, dan jaridar wasannin na kasar Italiya Fabrizio Romano ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.

Real Madrid zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Benfica a filin wasa na Santiago a ranar Laraba domin buga wasan zagaye na biyu na Play Off, a wasan farko da suka buga a Makon da ya gabata Madrid ta doke kungiyar ta kasar Portugal da ci 1-0.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *