Kebbi: Mun San Inda Ɗaliban Da Aka Sace Suke, Kuma Ana Kan Aikin Ceto Su



Sanata Garba Maidoki, wanda ke wakiltar Kebbi ta Kudu, ya ce yana da tabbacin cewa ‘yan mata 25 da aka sace a makarantar Sakandare ta Mata ta Maga, Jihar Kebbi, ba su bar yankin ba.

Ya yi fatan cewa za a dawo da su gida nan bada jimawa ba.

‘Yan bindiga sun kai harin a ranar Litinin, inda suka kashe mataimakiyar shugaban makarantar yayin da ta yi ƙoƙarin hana sj sace ɗaliban.

Tun daga lokacin, Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumomin tsaro da su ceto ɗaliban.

A ranar Laraba, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ziyarci al’ummar jihar inda ya yaba wa hukumomin tsaro kan ƙoƙarin da suke yi, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don dawo da ‘yan mata cikin aminci.

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da tafiyarsa zuwa ƙasashen waje don mayar da hankali wajen ceton ɗaliban.

Lamarin ya tayar da hankali sosai, inda UNICEF da sauran ƙungiyoyi suka nemi a ceto ‘yan matan lafiya.

Sace-sacen ɗalibai da kai wa makarantu hari a Nijeriya na ƙara ƙamari, ciki har da sace ‘yan makaranta a Chibok, Borno a shekarar 2014.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *