Nasarorin Kasar Sin Manuniya Ce Cewa, Abun Da Hakuri Da Sanin Ya Kamata Bai Kawo Ba, Nuna Karfi Ba Zai Kawo Ba
[ad_1]
Jiya Talata, cibiyar kimanta darajar tambura a duniya ta Brand Finance mai mazauni a birnin London, ta fitar da wasu rahotanni biyu: daya jeri ne na tambura mafiya karfi da daraja 500 a duniya, yayin da dayan rahoto ne da ya nuna cewa Sin ce kasa daya cikin manyan kasashe 10 da makin manufarta ta jan hankalin kasa da kasa cikin lumana ya karu.
Duk da ana ci gaba da samun sauye-sauye da rashin tabbas a duniya da kuma takkadamar cinikayya da ke ci gaba da kunno kai, kasar Sin na ci gaba da yin zarra da samun tagomashi kusan ta kowane bangare.
Mene ne sirrin kasar Sin?
Idan muka dubi rahoto na farko da ya nuna darajar tamburan kasar ta karu a duniya, kana yawansu cikin tambura 500 na duniya ya karu, za mu fahimci cewa wadannan nasarori sun samu ne daga kyawawan manufofin kasar na tallafawa da kare kamfanoninta da kuma ci gaba da bude kofarta da take yi ga kasashen waje. Maimakon nuna wariya da takure kamfanoninta da na ketare, kasar na samar da kyawawan muhalli na kasuwanci da cudanya, da karfafa wa kamfanoninta gwiwar shiga takara da tallafa musu domin tsayawa da kafarsu. Haka kuma manuniya ce cewa, duk wata takkadama ko bita da kulin da ake yi domin ganin faduwarta, sun yi rashin nasara.
Wani dalili shi ne, hangen nesa da kyakkyawan shiri. Misali, tun daga yanzu, cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da za a aiwatar tsakanin 2026 zuwa 2030, kasar Sin ta riga ta yi tanade-tanaden bunkasa sabbin masana’antu ko masana’antu masu tasowa da ma wadanda za su bullo a nan gaba. Wannan yana ba ’yan kasa kwarin gwiwar kirkire-kirkire da habaka kasuwancinsu, saboda sun san cewa, suna da goyon bayan gwamnati, kuma kullum burinta shi ne kare moriyarsu da samar musu damarmakin ci gaba.
Idan muka kalli rahoto na biyu, za mu fahimce cewa, kasar Sin ba ta shiga sharo ba shanu, ba ta matsin lamba, kuma ba ta neman iko da babakere. Karuwar makin ya nuna kyawawan sakamakon manufofinta na kyautata cudanya tsakaninta da kasa da kasa bisa girmama juna da adalci da taimakekeniya da cin moriyar juna. Ko cikin rahoton, an ambato shirye-shiryenta masu dogon zango kamar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da inganta cudanyar al’adu tsakaninta da kasa da kasa a matsayin misalai. Hakan ya nuna cewa kasa da kasa sun dawo daga rakiyar salon dangantakar kasashen yamma na gindaya sharudda da tsoma baki da babakere, haka kuma abun da hakuri da sanin ya kamata bai kawo ba, tashin hankali da matsi ba zai kawo ba.
[ad_2]
Source link