Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
[ad_1]
Matatar Man Fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur daga Naira 850 zuwa Naira 820 kan kowace lita, wanda sabon farashin zai fara aiki daga ranar 12 ga watan Agusta, 2025.
Matatar ta ce wannan ragin farashi yana cikin jajircewarsa na tallafawa ci gaban ƙasa, tare da tabbatar da cewa an samu isasshen mai a ko da yaushe.
Haka kuma, matatar ta sanar cewa daga ranar 15 ga watan Agusta, 2025, za ta fara amfani da sabbin manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) wajen rarraba mai a duk faɗin Nijeriya.
Wannan mataki na zuwa ne, yayin da mutane suka fara ƙorafin farashin man fetur na ci gaba da tashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link