Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

[ad_1]

Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta amince da kudirin da ke kayyade hukuncin daurin shekaru 14 ga malamai da aka samu da laifin cin zarafin dalibai mata a manyan makarantu.

Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke ci gaba da cewa, malamai suna amfani da damar dalibai masu neman maki ko wata alfarma sai su yi lalata da su – wannan matsalar ta tabbata a wani bincike da aka yi a jami’o’in Nijeriya tsawon shekaru, ciki har da binciken sirri na 2019 mai taken “Lalata don samun maki”, wanda ya fallasa cin zarafin da ake yi a wasu jami’o’i.

Dokar mai taken ‘Dokar Cin Zarafin Dalibai ta 2025’ (HB.1597), Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya) ne ya gabatar da ita domin amincewa.

Bamidele ya bayyana cewa, an gabatar da kudirin ne don kare dalibai daga duk wani nau’in cin zarafin jima’i da cin zarafi a rayuwar makaranta, wadda ta tanadi dokokin shari’a don aiwatar da hukunci da hukunta masu laifi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *