Sin Ta Kaddamar Da Bincike Game Da Wasu Matakai Da Amurka Ta Dauka
A yau Juma’a ne ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta sanar da aniyar kaddamar da binciken kariyar cinikayya mai nasaba da wasu ayyuka, da matakan kasar Amurka, wadanda ka iya illata tsarin sarrafa hajojin masana’antu da shigar da su sassan duniya, da ma kawo tsaiko ga cinikayyar hajoji marasa gurbata yanayi.
A ranar 12 ga watan nan na Maris agogon Beijing, ofishin wakilin cinikayya na Amurka, ya kaddamar da bincike karkashin sashe na 301 kan kasar Sin, da wasu karin rukunoni 15, bisa zarginsu da samar da hajoji fiye da kima, kana ofishin ya kuma kaddamar da wani bincike na daban karkashin sashe na 301, a ranar 13 ga watan na Maris kan kasar Sin, da karin wasu rukunoni 59.
A yau Juma’a, kakakin ma’aikatar cinikayya ta Sin ya amsa tambayar da aka yi game da hakan, yana mai bayyana matukar rashin gamsuwar kasar Sin da wadannan matakai biyu. Kakakin ya ce domin kare moriyar kamfanonin kasar Sin da batun ya shafa, ma’aikatar ta kaddamar da bincike biyu bisa tanadin dokar cinikayyar waje ta Sin, da ka’idojinta na bincike kan kariyar cinikayyar waje.
Har ila yau, ma’aikatar cinikayyar Sin za ta zurfafa bincike daidai da tanadin doka da ka’idoji, tare da aiwatar da matakai masu nasaba da abubuwan da aka gano. (Saminu Alhassan)