An yi wa Ladani yankan rago a masallaci a Kano
[ad_1]
Wani matashi ya yi wa wani Ladani mai shekaru 70 yankan rago a wani masallaci a unguwar Hotoro Maraba da ke kano.
Al’ummar unguwar sun shiga damuwa bayan matashin da ake zargi ya yanke maƙogwaron dattijon a lokacin Sallar Asubahin ranar Litinin.
An ruwaito cewa da misalin ƙarfe 5 na asuba, maharin ya far wa Ladanin, ya rinjaye shi, ya yanka wuyansa, ya bar shi cikin jini.
Lamarin ya jawo hankalin maƙwabta, suka far wa maharin da kulake da wuƙa, amma ba su iya shawo kansa ba, ya tsere, ya shiga wani gida.
Wasu azauna unguwar sun ce matashin ya iske ladanin wasu mutane uku a masallacin, inda ya nemi a tayar da sallah, amma ladanin ya bayyana masa cewar lokaci bai ƙarasa ba.
Daga nan ya zaro wuƙa daga aljihunsa ya soka masa a maƙogwaro harma aka yi zargin ya cire maƙogoron marigayin ya sanya a leda.
Wannan ya sa ’yan unguwar suka ce da wa Allah Ya hada su in ba shi ba, amma ya suka kasa kama shi, inda ya tsere ya shiga wani gida, inda ya soka wani matashi mai shekaru 26, wanda yake barci a dakinsa wuka a fuska.
Daga karshe fusatattun mutanen unguwar suka kamo shi, suka lakaɗa masa duka, har ya ce ga garinku nan. Sun kuma far wa gidansa domin cinna masa wuta.
Rahotanni sun ce ’yan sanda sun isa wurin domin kwantar da tarzomar da ke shirin ɓarkewa bayar matasa sun yi yukurin kone gidan dan uwan wanda ake zargin.
’Yan sanda sun mika gawara ladanin ga iyalansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Islama ya tanadar, amma sun ci gaba da rike gawar wanda ake zargin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link