An Yi Zama Na Biyu Na Taron Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin
[ad_1]
A yau Litinin, aka yi zama na 2 na taro na 4 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) ta 14.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar da na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ne suka halarci taron.
Yayin zaman, shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar Zhao Leji, ya gabatar da rahoton aikin kwamitinsa
Shi ma shugaban hukumar koli mai karbar korafe-korafen jama’a Ying Yong, ya gabatar da rahoton aiki na hukumar, wanda ya bayyana cewa, adadin mutanen da aka yanke wa hukunci kan laifukan da suka shafi cin zarafin kananan yara ya ragu da kaso 2.2 bisa dari, yayin da adadin yaran da aka yanke wa hukunci bayan aikata laifuka, ya ragu da kaso 9.8 bisa dari.
A rahoton da ya gabatar ga majalisar, shugaban kotun koli na kasar Zhang Jun, ya ce tsarin shari’a ta kasar Sin ba ta lamunci cin zarafin yara ba ko kadan. Ya ce a shekarar 2025, an kammla sauraron kararraki 40,000 da suka shafi zarafin yara, adadin da ya ragu da kaso 1.8 bisa dari kan mizanin shekara-shekara, kana kuma an yanke wa mutane 44,000 hukunci.
A cewar rahoton kotun kolin, a bara, jimilar kararraki 25,000 na laifukan da suka shafi kafar intanet aka kammala sauraro, adadin da ya ragu da kaso 62 kan mizanin shekara-shekara, kana an yanke wa mutane 38,000 hukunci.
Har ila yau a shekarar 2025, kotunan kasar Sin sun kammala sauraron kararraki 36,000 kamar na cin hanci da rashawa wadanda suka shafi ma’aikatan gwamnati, adadin da ya karu da kaso 22.4 kan mizanin shekara-shekara.
Shi kuwa rahoton kwamitin dindindin na majalisar NPC ya bayyana cewa, domin karfafa dokokin da suka shafi tattalin arziki, ya zartar da dokar kyautata wa bangarori masu zaman kansu, wadda ta zayyana ka’idojin rashin nuna wariya da tabbatar da takara cikin adalci da ba da kariya da samar da ci gaba na bai daya.
Haka kuma, ya sake bitar dokar da ta shafi harkokin teku da ta warware sabani da ta cinikayya da kasa da kasa, ta yadda za su yi daidai da dokokin kasa da kasa da kuma kara kyautata manufar bude kofa ta kasar Sin.
A cewar rahoton, domin inganta dokar yaki da cin hanci ta kasa, kasar Sin za ta yi doka kan yaki da cin hanci tsakanin kasa da kasa. Bugu da kari, za ta inganta tsara dokokin da suka shafi kadarorin gwamnati, a matsayin wani bangare na kokarin samar da tattalin arziki irin na gurguzu mai matukar inganci. (FMM)
[ad_2]
Source link