A gaggauta sakin ’yan Najeriya 42 da aka kama a Mozambique — NiDCOM

[ad_1]



Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta buƙaci mahukuntan ƙasar Mozambique su gaggauta sakin ’yan Najeriya 42 da aka kama a ƙasar ba tare da bayyana takamaiman laifin da suka aikata ba.

Shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana damuwa kan lamarin, tana mai cewa kama ’yan Najeriya ba tare da tuhuma ba abin takaici ne kuma ya kamata a sake su ko kuma a gurfanar da su a gaban kotu idan sun aikata wani laifi.

A wata sanarwa da kakakin NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, Dabiri-Erewa ta ce abin damuwa ne yadda aka kama ’yan Najeriya kaɗai a yayin wani samame da aka kai a wata kasuwar sayar da kayan gyaran motoci.

Ta ce rahotanni sun nuna cewa an bar ’yan kasuwa na wasu ƙasashe da ke wurin, yayin da aka kama ’yan Najeriya kaɗai, lamarin da ta ce na iya nuna wariya ko nuna ƙyama ga ’yan ƙasar.

“Abin takaici ne a ji cewa ’yan Najeriya kaɗai aka je aka kama,” in ji ta. “Idan har sun karya doka, ya kamata mahukunta su gurfanar da su a gaban kotu.”

NiDCOM ta kuma ce bayanan da ta samu sun nuna cewa waɗanda aka kama suna zaune a Mozambique bisa ƙa’ida, kuma babu wata tuhuma da Ofishin Jakadancin Najeriya ya samu a kansu.

“Kamen ’yan Najeriya kaɗai da aka yi farat ɗaya yana nuni da cewa an yi kamen ne saboda nuna ƙyama ko wariya ga ’yan ƙasar Nijeriya,” in ji Dabiri-Erewa.

Hukumar ta kuma ambato rahotannin da ke cewa an doki wasu daga cikinsu lokacin kamen, an kwashe musu kayayyakinsu, sannan wasu sun kamu da rashin lafiya a gidan yari kuma suna buƙatar kulawar likitoci.

Dabiri-Erewa ta buƙaci mahukuntan Mozambique su tabbatar da tsaro da lafiyar ’yan Najeriyar da aka tsare yayin da ake ƙoƙarin warware matsalar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *