Daga Ranar 1 Ga Maris, Za A Fara Hutun Zango Na Biyu Na Makarantu A Kano

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar Lahadi, 1 ga Maris, a matsayin ranar fara hutun Eid al-Fitr ga dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu na firamare da na sakandire a jihar.

Sanarwar, wacce aka fitar a ranar Laraba ta hannun Daraktan Wayar da Kan Jama’a, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Musbahu Aminu Yakasai, ta yi daidai da kalandar karatu ta 2025/2026 da aka amince da ita, wanda ke nuna cewa zango na biyu zai ƙare a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu.

“Makarantun jeka-ka-dawo da na kwana a duk faɗin Jihar Kano za su fara hutun Sallah daga 1 ga Maris.

“Ana kira ga iyaye da masu jiɓintar lamarin ɗalibai su tabbatar sun mayar da ɗaliban makarantun kwana gida kafin safiyar Juma’a, 27,” in ji Yakasai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *