Babu kotun da za ta iya dakatar da tsige Fubara — Majalisar Dokokin Ribas

[ad_1]



Majalisar Dokokin Jihar Ribas, ta ce babu kotun da za ta iya hana ta gudanar da kundin tsarin mulki, ciki har da yunƙurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

Majalisar ta zargi wasu mutane da ke da alaƙa da ɓangaren zartarwa da shirin neman umarnin wata babbar kotu da ke Fatakwal domin hana ’yan majalisar tsige gwamnan jihar.

Majalisar ta ce irin wannan yunƙuri ya saɓa da doka da kuma Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Ta buƙaci jami’an da aka riga aka miƙa musu takardun zargin manyan laifuka su mayar da martani yadda doka ta tanada, maimakon ƙoƙarin daƙile Majalisar ta hanyar amfani da kotu.

“Mun samu bayanai cewa wasu mutane na shirin amfani da kotuna da ke Fatakwal domin dakatar da Majalisar Dokokin Jihar Ribas daga yin aikinta ba bisa doka ba,” in ji Dakta Enemi Alabo George, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar.

“Abin da ake buƙata kawai shi ne jami’an da aka aike wa takardun zargin manyan laifuka su amsa su dalla-dalla, ba wai su yi ƙoƙarin karya doka ko kai wa Majalisar hari ta hannun wasu ba,” in ji shi.

Majalisar ta yi kira ga duk masu hannu a lamarin da su mutunta kundin tsarin mulki da bin doka, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya da bin ƙa’ida.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *