An kama wani mutum kan zargin kashe mai gidan da yake haya a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum mai suna Bello Abubakar, mai shekaru 37, bisa zargin kashe mai gidan da yake haha, Maryam Hassan, mai shekaru 38, a Unguwar Arawa a cikin garin Gombe.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata 3 ga watan Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 6 na safe.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce wani mutum ne ya kai rahoto cewa an ga Maryam Hassan kwance a gaban gidanta cikin jini.

’Yan sanda sun gaggauta zuwa wajen, inda suka kai ta asibiti, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

Bincike ya kai ga kama Bello Abubakar, wanda ɗan haya ne a gidan marigayiyar, domin yi masa tambayoyi.

’Yan sanda sun ce sun samu wasu abubuwa a hannun wanda ake zargi da ake tunanin an yi amfani da su wajen aikata laifin, ciki har da turmi, kujera, bokiti, riga mai ɗauke da jini, da kuma wayar marigayiyar.

DSP Abdullahi ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin.

Ya ce an miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya buƙaci jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da bayanai a kan lokaci domin inganta tsaro a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *