Amurka ce kaɗai ke da ƙarfin tabbatar da tsaron Greenland — Trump

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa ƙasarsa ce kaɗai a duniya ke da ƙarfin tabbatar da tsaron yankin Greenland, mallakin ƙasar Denmark, yana mai cewa babu wata ƙasa mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO da za ta iya kare tsibirin yadda ya kamata.

Trump ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a taron tsara manufofin tattalin arziki na duniya da aka gudanar a Davos, Switzerland.

A yayin taron, Trump ya yi kira da a gaggauta gudanar da taro kan niyyar ƙasarsa ta mayar da yankin Greenland ƙarƙashin ikonta.

Sai dai Denmark, wacce ita ma mamba ce a ƙungiyar tsaro ta NATO, ta soki wannan matsayi, tana mai jaddada cewa Greenland wani ɓangare ne na ƙasarta.

Shugaba Trump, wanda shugabannin Turai ke sukar kalamansa, ya mayar musu da martani inda ya ce nahiyar Turai ba ta da ƙarfin tafiyar da harkokin tsaron Greenland yadda ya kamata.

Ya ce: “Ina girmama mutanen Greenland da ’yan Denmark sosai. Amma kowace ƙasa da ke da kujera a NATO na da alhakin kare kanta.

“Gaskiyar magana ita ce, babu wata ƙasa ko ƙungiya da za ta iya kare Greenland sai Amurka. Mu ƙasa ce mai ƙarfi, kuma ƙarfinmu ya fi yadda mutane da dama ke zato.”

A bayan nan dai Trump ya ci gaba da jajircewa kan batunsa na son mallakar yankin Greenland, inda a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana cewa Amurka na son tsibirin ne kan dalilai na tsaro.

Greenland yanki ne mai ’yanci, da ke mulkin kansa a ƙarƙashin masarautar Denmark — kuma mamba a Tarayyar Turai da NATO.

Yanzu shugaba Trump ya dogara ne kan ƙawayen Denmark a waɗannan ƙungiyoyi domin watsi da Copenhagen don ganin Amurka ta karɓi ikon Greenland, ko kuma su fuskanci matsanancin haraji kan kayayyaki da za su shigar Amurka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *