Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes

[ad_1]



Fitaccen attajirin nan, Aliko Dangote ya ci gaba da riƙe kambinsa na mutum mafi arziƙi a nahiyar Afirka, inda dukiyarsa ta kai dala biliyan $24.4, a cewar sabuwar ƙididdigar da mujallar Forbes ta fitar a bana.

Wannan ya sanya shi zama mutum na 88 a jerin masu kuɗin duniya, inda ya rike wannan matsayi da tazara mai nisa a kan sauran attajiran Najeriya.

Abdulsamad Rabiu wanda ya mallaki rukunin kamfanin BUA, shi ne ya biyo bayansa da dukiyar da ta kai dala biliyan $7.2, wanda ya sa shi zama attajiri na 516 a duniya.

Sai kuma Mike Adenuga da dukiya mai darajar dala biliyan $6.3 wanda ke rike matsayi na 592 a duniya, sannan Femi Otedola wanda ke da dala biliyan $1.5, ya kuma tsaya a matsayi na 2424 a duniya.

Tun daga shekarar 2008 ne Dangote ya fara bayyana a jerin masu kuɗin duniya na Forbes.

Daga shekarar 2011 zuwa yau, ya ci gaba da zama mutum mafi arziki a Afirka, inda ya riƙe wannan matsayi na tsawon shekaru 14 a jere.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *