An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da su a ƙauyen Euga da ke Ƙaramar hukumar Toro a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da majiyar PUNCH Metro ta ruwaito ranar Laraba.
A cewar sanarwar, aikin ceton waɗanda aka kuɓutar ya biyo bayan kiran gaggawa da wani ɗan unguwar ya yi ga hukumar ne.
Wakil ya ce, “A ranar 29 ga Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 12:01 na tsakar dare rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta samu kiran gaggawa daga wani ɗan banga na unguwar, inda ya ba da rahoton harin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai ga sace wasu maza uku daga ƙauyen Euga, a Ƙaramar hukumar Toro da suka haɗa da: Idi Umar da Idi Lawan da Musa Lawal.”
Ya ƙara da cewa, rundunar ’yan sandan ta yi gaggawar tattara jami’an rundunar ’yan sandan yankin Toro, na babban ofishin jami’an Toro da na ofishin Nabordo, tare da jami’an tsaro na yankin domin kai ɗauki ga lamarin.
“Rundunar haɗin gwiwa ta yi nasarar bin diddigin waɗanda ake zargin zuwa wajen ƙauyen tare da gudanar da aikin ƙwararru wanda ya kai ga ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Wakil ya ƙara da cewa, an kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a wannan lamarin.”
Waɗanda ake zargin sun haɗa da: Abubakar Usman da Adamu Alo da Abubakar Aliyu da Umar Habu da Abubakar Mamman Abubakar da kuma Shehu Samb.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link