NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe
[ad_1]
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Gombe ta ce ta lalata wata babbar gonar Tabar wiwi a Karamar Hukumar Kaltungo a jihar Gombe.
Hukumar ta kuma ce ta kama miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025.
Kwamandan Hukumar a jihar, Mallam Maijama’a Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar kulla zumunci da ya kai wa Darakta-Janar na kafar yada labarai mallakar jihar Gombe (GMC), Ibrahim Isa.
Ya ce an kama mutum 69 maza da mata da suke kokarin shigar da miyagun kwayoyi cikin jihar a wasu lokuta.
Muhammad ya kuma ce hukumar na amfani da dabarun rage samarwa da rage bukatar miyagun kwayoyi, tare da kira ga karin hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.
Daga nan sai ya gode wa gwamnatin Jihar bisa bayar da motocin aiki guda biyu da gyaran ofishin hukumar, da inganta cibiyar farfado da masu shan miyagun kwayoyi
A nasa jawabin, Daktan kafar yada labaran, Ibrahim Isa, ya tabbatar wa NDLEA da goyon bayan kafar ta GMC, ciki har da bayar da lokacin watsa shirye-shirye kyauta, tare da alkawarin ci gaba da yin aiki tare wajen yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link