’Yan sanda sun kama matashi kan zargin aikata fashi a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi mai shekara 18 bisa zargin aikata fashi da makami a jihar.

An kama shi ne a garin Kwadon bayan samun sahihin bayani daga jama’a.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama matashin ne ranar 9 ga watan Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

Hakazalika, ya ce an samu ƙunshi ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.

Bincike ya nuna cewa matashin na cikin mutanen da ’yan sanda ke nema game da aikata fashi da makami, waɗanda ake shari’arsu a babbar kotun jihar.

A cewar DSP Abdullahi, matashin ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka kai hare-haren.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Bello Yahaya, ya umsrci a miƙa shi zuwa sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike kafin gurfanar da shi a kotu.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba ta bayanai da za su taimaka wajen yaƙar laifuka a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *