An tsinci tagwaye a cikin bola a Filato

[ad_1]



Mazauna yankin “Special Site” da ke Karamar Hukumar Pankshin a Jihar Filato sun bayyana alhini da ɓacin rai bayan gano wasu jarirai tagwaye  a cikin bola a yankin.

Gano jariran, wanda ya faru a ranar Laraba, ya bar mazauna yankin cikin damuwa, inda wasu suka bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi da kuma ban tsoro.

Jariran, waɗanda aka ƙiyasta sun kai kimanin watanni biyar kuma aka gano mace da namiji ne, an ce, an same su ne a cikin leda a wani wurin zubar da shara da ke bayan gidajen mutane.

Wani mazaunin yankin mai suna Enman Danladi, wanda gidansa yake kusa da bolar, ya bayyana yadda aka gano su:

“Ni direban tasi ne mai zirga-zirga a cikin gari. Lokacin da na dawo daga aiki, sai wani mutum da yake noman rani a bayan gidana ya zo ya sanar da ni abin da ya gani,” kamar yadda ya bayyanawa  Daily Trust.

“Ya ce ya lura da wani kare yana shinshina wata leda, yayin da ƙudaje ke ta yawo a kanta. Wannan ya ba shi masaniya. Bayan ya kora karen, sai ya duba ledar ya ga ashe tagwaye ne, sannan ya rugo da gudu ya faɗa mini.”

A cewarsa, nan take ya sanar da sauran mazauna yankin, inda mutane kusan takwas suka taru a wurin. “Dukanmu mun je can kuma mun tabbatar da abin da ya gani. Gaskiya abin ya tayar mana da hankali sosai,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *