Bafarawa ya sauya sheƙa zuwa jami’yyar APC

[ad_1]



Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

Bafarawa tare da magoya bayansa sun bayyana komawa jam’iyyar APC ne, a ranar Laraba, a babban ɗakin taro na gidansa da ke Jihar Sakkwato.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa dangantakar magoya bayansa da jam’iyyar APC za ta kasance ne ta hannun shugaban ƙungiyar magoya bayansa, Farfesa Hamza Maishanu, da shugabannin jam’iyyar.

Ya ce ya daina siyasar neman kujera, kuma ba shi da sha’awar tsayawa takara a kowace kujera.

Sai dai ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin magoya bayansa sun samu nasara a siyasa.

“Akwai wasu ’yan siyasa masu bin inda maslaha ta dosa, duk inda ta juya can suke bi. A lokacin da nake gwamna ban fahimci irin wannan hali ba sai bayan na sauka daga mulki,” in ji Bafarawa.

Komawar Bafarawa jam’iyyar APC ba abin mamaki ba ne, duba da yadda dangantakarsa da jam’iyyar ke ƙara ƙarfafa a jihar.

A baya-bayan nan ya sha yabon Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu.

Hakan ya sa mutane da dama suka yi hasashen cewa zai koma APC, kamar yadda ta tabbata a yanzu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *