APC Ba Ta Da Ƙarfin Da Za Ta Lashe Zaɓen 2027 Ba Tare Da Kwankwaso Ba

[ad_1]


Shugaban NNPP a Jihar Kano, Alhaji Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce Jam’iyyar APC ba ta da karfin siyasa na lashe babban zaben 2027 ba tare da tasirin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.

Dungurawa ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Alhamis a Kano, wanda aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar NNPP.

Ya yi zargin cewa, jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa da jiha “ta hautsine ta rasa alkibla,” hakan ne yasa ta ke ta bikon ɗan takarar shugaban kasa na NNPP.

“Waɗannan mutanen, APC suna da rauni kuma sun ruɗe. Sun san ba tare da Kwankwaso ba, ba za su yi nasara a 2027 ba,” in ji shi. “Suna ci gaba da gaya wa jama’a cewa, suna tattaunawa da shi. Suna bukatarsa, amma shi (Kwankwaso) hankalinsa, yana ga samar da walwala da jin daɗin ‘yan Nijeriya ne kaɗai.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *