CAF Ta Ci Tarar Senegal Da Morocco Kan Haddasa Rikici A Wasan Ƙarshe Na Gasar AFCON

[ad_1]

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ci tarar Senegal da Morocco bayan rikicin da ya faru a wasan ƙarshe na AFCON ta 2025 a birnin Rabat.

An ci tarar hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal da dala 615,000 saboda rashin ɗa’a da ’yan wasanta, jami’ai da magoya bayanta suka aikata.

  • Firaministan Kasar Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
  • Ana Maraba Da ‘Yan Jarida Na Cikin Gida Da Na Ketare Ga Taron NPC da CPPCC Da Sin Za Ta Gudanar

Haka kuma an ci tarar kocin Senegal, Pape Bouna Thiaw, da dala 100,000.

An ci tarar hukumar ƙwallon kafa ta dala 315,000 sakamakon hatsaniyar magoya bayanta, rashin ɗa’a daga yara masu ajiye ƙwallo a bayan fili, da kuma jami’an da suka tare wajen duba na’urar VAR.

Haka kuma an ci tarar ɗan wasan tsakiyar Morocco, Ismaël Saibari, da dala 100,000.

An kuma dakatar da ɗan wasan bayan Morocco, Achraf Hakimi wasanni biyu.

CAF ta ce wannan hukunci gargaɗi ne mai tsauri.

Ta kuma jaddada cewa dole ne a mutunta alƙalan wasa, a kiyaye gaskiya da ladabi a ƙwallon ƙafa ta Afirka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *