Ba za mu aminta da zaɓen da Amupitan zai jagoranta ba — Majalisar Shari’a

[ad_1]



Majalisar Shari’a ta Najeriya (SCSN), ta bayyana cewa Musulmi ba za su aminta da kowane irin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta gudanar ƙarƙashin shugabanta, Farfesa Joash Amupitan ba.

Majalisar ta bayyana haka ne yayin laccar shekara-shekara gabanin watan azumin Ramadan a Abuja, inda ta nemi a sauke Amupitan saboda rashin amincewa da adalci da gaskiyarsa.

Shugaban majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya ce rashin amincewar ya samo asali ne, sakamakon zargin da Amupitan ya yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya.

“Muna buƙatar a sauke shugaban INEC nan take a gurfanar da shi a gaban shari’a kuma muna bayyana cewa ba za mu amincewa da kowane zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin mutumin da bashi da gaskiya ba,” in ji Umar.

Ya ƙara da cewa, “Dole ne a kiyaye ingancin dimokuraɗiyya. Duk wanda rashin gaskiya ya rufe masa ido ya kamata ya yi murabus, ko kuma gwamnati ta sallame shi ko ta tilasta masa yin ritaya.”

Umar, ya kuma ƙaryata batun yi wa “Kiristoci kisan ƙare dangi” inda ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan labaran na ƙara raba kan al’umma kuma suna barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Ya ce majalisar tana goyon bayan duk wani ƙoƙari da ke ƙalubalantar naɗin Amupitan kuma za ta tallafa wa duk wani yunƙuri na doka wajen tantance sahihancin naɗinsa.

Majalisar ta kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta Tarayya da ta tabbatar an yi bincike da sa ido kan dokoki da manufofi, tare da kira ga gwamnati da ta kare duk ’yan Najeriya ta hanyar samar da tsaro da sulhu cikin lumana.

Umar, ya jaddada cewa dole ne a kiyaye hakkokin Shari’a ga Musulmi, yayin da ya tabbatar cewa dokokin Shari’a ba sa take haƙƙin Kiristoci ko sauran addinai.

Majalisar ta soki shigar ƙasashen waje cikin al’amuran cikin gida da duk wani yunƙuri na canza dokokin da aka amince da su ba tare da izinin majalisa ba, tare da jaddada cewa tattaunawa a bainar jama’a da nazarin dokoki yana da muhimmanci.

Wani jami’in INEC, wanda ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce hukumar ba ta da ikon sauke Amupitan.

“Da alama ba aikin hukumar ne amsa irin waɗannan kiranye-kiranye ba. Duk wata amsa ya kamata ta fito daga wanda ya naɗa shi,” in ji jami’in.

Jami’in ya ƙara da cewa INEC tana mayar da hankali ne kawai kan gudanar da zaɓe cikin gaskiya, adalci da inganci a faɗin ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa dukkanin manyan shawarwari a INEC ana yinsu ne tare da haɗin gwiwar dukkanin kwamishinonin ƙasa 12, kuma hukumar ba za ta bari a ɗauke hankalinta daga kan gudanar da aikinta ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *