Yadda Tayar Jirgin Sama Ta Ɓalle Bayan Tashinsa A Amurka

[ad_1]

An fara gudanar da bincike kan yadda ɗaya daga cikin tayoyin jirgin British Airways da ta ɓalle ta faɗo ƙasa jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na Las Vegas, a Amurka.

An ɗauki lamarin kai-tsaye a bidiyo, wanda daga bisani aka yaɗa a kafofin sada zumunta, lamarin da ya jawo hankalin mutane da dama.

  • Kamfanonin Finland: Sin Za Ta Zama Babban Injin Samar Da Ci Gaba A Gare Mu
  • Gwamna Yusuf Zai Yi Nadamar Barinmu – Kwankwaso

Jirgin, samfurin Airbus A350, ya ci gaba da tafiya duk da matsalar, kuma ya sauka lafiya a birnin Landan bayan kusan sa’o’i tara da tashinsa.

Kamfanin British Airways ya ce babu wani rahoton jikkatar fasinjoji ko ma’aikatan jirgin sakamakon lamarin.

Haka kuma, ya ce jirgin na ɗauke da fasinjoji da ma’aikata da dama a lokacin da abin ya faru.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya jaddada cewa tsaro da lafiyar fasinjoji su ne babban abin da ya fi bai wa muhimmanci, kuma zai ba da cikakken haɗin kai ga hukumomin sufurin jiragen sama wajen binciken musabbabin matsalar.

Hukumomi a Amurka da Birtaniya na sa ran binciken zai taimaka wajen gano ko matsalar ta samo asali ne daga lalacewar kayan aiki ko kuskuren fasaha, domin hana faruwar makamancin haka a nan gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *