CBN Ta Amince Wa Bankin Masana’antu Buɗe Sashin Bankin Da Babu Riba

[ad_1]

Bankin Masana’antu na Nijeriya (BoI) ya samu amincewar Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin fara gudanar da ayyukan bankin da babu riba (Non-Interest Banking Window), matakin da ke faɗaɗa tsarin bayar da kuɗaɗensa ga jama’a.

Daraktan Janar na BoI, Dakta Olasupo Olusi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar 8 ga Fabrairu, 2026. Ya ce amincewar ta ba bankin damar fara samar da tsarin kuɗi da ba ya karɓar kuɗin ruwa, wanda ke dogaro da kadarori tare da rabon asara tsakanin ɓangarorin da ke hulɗa.

  • Sabbin Nau’o’in Masana’antun Ba Da Hidimomi Suna Karuwa
  • An Yi Taron Dandalin Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Beijing

A cewarsa, matakin zai ƙarfafa rawar da BoI ke takawa wajen bunƙasa masana’antu da samar da damar neman kuɗi ga ɓangarorin kasuwanci da ba su da cikakkiyar dama, musamman waɗanda ke da tasiri ga tattalin arziki.

Olusi ya bayyana amincewar a matsayin wani muhimmin mataki a cikin tsarin bunƙasa bankin na dogon lokaci, yana mai cewa zai taimaka wajen samar da hanyoyin kuɗi na musamman da suka dace da manufofin ci gaban masana’antu mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa amincewar na nuna amincewar CBN da tsarin gudanarwa da kuma jajircewar BoI wajen bin ƙa’idojin bayar da kuɗi cikin gaskiya da ɗorewa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *