Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya

[ad_1]



Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya.

Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja.

Maharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic.

Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.

Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa, musamman a Arewa.

A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya nuna damuwarsa.

“Abin takaici ne sosai. Har yaushe za a ci gaba da rasa rayuka ba tare da an ɗauki matakin gaggawa ba?”

Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta ɗauki tsauraran matakai.

Ya kuma buƙaci ƙarin tsaro a makarantu domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *