Zan Sauya Sheka In An Bani Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa Ko Mataimaki – Kwankwaso
[ad_1]
Daga Salim Sani Shehu
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ɗan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya ce zai i ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar bisa sharaɗin idan aka ba shi tikitin takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa kafin babban zaben 2027.
Kwankwaso ya yi Allah wadai da shirin sauya shekar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano zuwa Jam’iyyar APC, yana mai bayyana matakin a matsayin cin amana.
- AFCON 2025: Yadda Wasannin Zagayen ‘Yan 16 Za Su Kasance
- Sauya Sheka: Gwamna Abba Ya Yi Daidai
Kwankwaso ya sake nanata alƙawarin NNPP ga akidar siyasarsa (Kwankwasiyya) wanda ya ce, ya mayar da hankali kan tallafawa talakawa da matasa ta hanyar wadata su da aiki da ilimi da inganta tattalin arziki da inganta kiwon lafiya da ci gaban noma.
Da yake tsokaci game da shirin sauya shekar gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa APC, Kwankwaso ya ce, “Wannan darasi ne ga dukkanmu, ba mu taɓa tunanin cin amana ba. Abu mafi zafi shi ne, bayan duk abin da muka yi don ceto Kano daga Ganduje da APC, yanzu kun mayar masa Kano kyauta,” in ji Kwankwaso.
Ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu su yi addu’a.
[ad_2]
Source link