An ayyana kawo ƙarshen annobar Marburg a Habasha

[ad_1]



Gwamnatin Habasha ta ayyana kawo ƙarshen annobar cutar Marburg — wata ƙwayar cuta mai kama da Ebola — kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar a ranar Litinin.

Kafin yanzu, annobar ta yi ajalin mutane tara daga cikin mutum 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan gano ɓullar ta karon farko a tsakiyar watan Nuwamba a garin Jinka, da ke kimanin kilomita 430 kudu maso yammacin babban birnin ƙasar, Addis Ababa.

A wani saƙo da ta wallafa a shafin X, WHO ta ce: “Habasha ta sanar da kawo ƙarshen annobar cutar Marburg karon farko a tarihinta, bayan bincike mai tsanani da aka gudanar wanda aka tabbatar babu wani sabon mai ɗauke da ƙwayar cutar.

“A (Habasha) an shawo kan annobar cikin ƙasa da watanni uku ta hanyar matakan gwamnati, tare da goyon bayan WHO.”

Habasha ita ce ƙasa ta biyu mafi yawan jama’a a Afirka, inda ake ƙiyasta tana da mutane kusan miliyan 130.

A shekarun baya-bayan nan, wasu ƙasashen Afirka da dama sun fuskanci ɓullar cutar Marburg, ciki har da Ghana, Equatorial Guinea, Afirka ta Kudu da Tanzaniya.

Mahukunta sun ce cutar Marburg tana haddasa zazzaɓi mai tsanani, kuma tana da saurin yaɗuwa, wadda mutane ke ɗaukar ta daga wasu nau’o’in jemagu, sannan daga bisani ta riƙa yaɗuwa tsakanin mutane ta hanyar ruwan jiki.

Har yanzu babu allurar rigakafi ko maganin kashe ƙwayar cutar Marburg da aka amince da shi, sai dai ƙarin ruwan jiki da kuma kula da alamomin cutar na taimakawa wajen ƙara damar tsira.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *