PDP za ta sake farɗaɗowa idan shugabanninta suka cire girman kai — Anenih
[ad_1]
Tsohuwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP, Iyom Josephine Anenih, ta ce jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi idan shugabanninta suka cire girman kai suka mayar da hankali kan yi wa jama’a hidima.
Ta bayyana haka ne yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a ranar Asabar.
Ta ce har yanzu ’yan Najeriya da dama suna sa ran jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi domin yi musu jagoranci.
Anenih, ta yi gargaɗin cewa PDP na iya zama tarihi idan ba a gyara matsalolinta ba.
“Idan ba mu fuskanci matsalolinmu ba, PDP za ta zama tarihi, labarin yadda sakaci da girman kai suka lalata babbar jam’iyyar siyasa mafi girma a Afirka,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa rikicin cikin gida, rashin ladabi, da cin amanar juna ne suka raunana jam’iyyar.
“Mambobinmu su ne ƙarfin PDP na gaskiya. Sun yi tsayin daka duk da matsalolin da ake fuskanta. Wannan babban taro dole ne ya girmama jajircewarsu,” ta ce.
Anenih, ta roƙi shugabannin jam’iyyar su kawo ƙarshen rigingimu da suka dabaibaye ta hanyar haɗa kai don sake gina jam’iyyar.
Ta ce Najeriya na buƙatar jam’iyyar adawa mai ƙarfi, wacce za ta kawo ƙarshen talauci da rashin tsaro da ake fama da su.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link