An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum

[ad_1]



Wasu da ake kyautata zaton ’yan bangar ’yan siyasa ne sun kashe wasu yara biyu na Zannah Jaridama Bornoye wani mai goyon bayan Gwamnan Borno Babagana Zulum, da na maƙwabcinsa kwanaki kaɗan bayan da Zannan ya fito ƙarara ya caccaki waɗanda ake zargin ’yan siyasa ne a jihar da ke zagon ƙasa ga gwamnatin Zulum.

Kamar yadda rahoton ke nunawa Zannah Jaridama, wanda ya zargi wasu manyan mutane da munafunci da zagon ƙasa ga gwamnatin mai gidansa Gwamna Zulum, ya koka a cikin wani faifan bidiyo.

Yana cewa, wasu mutane na kusa da gwamnan suna nuna cewa masu biyayya ne tare da wadatar da kansu da kwangiloli, muƙamai da dukiyar gwamnati ba tare da nuna kishin gaskiya ga jama’a ko hangen nesa na gwamna ba.

Ya koka da cewa, yayin da Farfesa Zulum ke ɗaukar nauyin mulki da ayyuka da yawa daga cikin waɗanda ke da’awar cewa su ne masu yi masa biyayya, yadda suke gina manyan gidaje na alfarma sai ga shi suna zagon ƙasa ga gwamnatinsa.

Daga bisani ya jajirce kan duk wanda ya ji bai masa daɗi ba ya kai shi kotu, yana mai cewa zai bayyana sunayensu a bainar jama’a nan gaba kaɗan.

Majiyar na cewar, bayan kusan awanni 24 bayan kalaman nasa, wannan kisan gilla na kashe waɗannan yara ya afku.

Waɗannan yara biyu da aka yi wa kisan gilla sun haɗa da Mama yarinya ’yar shekara 14 da Anwar ɗan wata 28 waɗanda daga farko aka neme su aka rasa waɗanda ana zargin an sace su ne a ƙofar gidansu, amma kwanaki kaɗan sai aka tsinci gawarwakin yaran da sanyin safiyar yau Alhamis a boot ɗin motarsa.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Borno, Nazir Abdulmajid wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gano gawarwakin yaran a cikin boot ɗin a wata tsohuwar motarsa ​​da aka kulle a harabar gidan.

A yanzu dai haka an baza jami’an rundunar ’yan sanda inda lamarin ya faru kuma an ɗauki hotuna, kuma an kai gawarwakin su zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin a tantance ko an yi garkuwa da su ne aka kashe su ko kuma sun shiga boot ne suka kulle kansu har suka mutu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *