Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran
[ad_1]
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ƙaƙaba harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wata ƙasa da ta ci gaba da kasuwanci da Iran.
Ya ce matakin zai fara aiki nan take.
- Barin Almakashin Tiyata Acikin Ciki: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Ma’aikatan Asibiti 3
- Sojoji Sun Kama Mutane 2 Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Taraba
Trump ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, amma bai yi cikakken bayani kan yadda za a aiwatar da harajin ba.
Ana ganin barazanar ta shafi ƙasashe irin su China, Rasha, Indiya da Turkiyya.
China ta soki wannan mataki, inda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajenta ta ce barazanar ba za ta amfani Amurka ba, kuma za ta ƙara dagula harkokin cinikayyar duniya.
Barazanar na zuwa ne yayin da dangantakar Amurka da wasu manyan ƙasashe ke ƙara taɓarɓarewa.
Trump ya kuma yi barazanar ɗaukar matakan soji kan Iran idan ta ci gaba da shirye-shiryen makamin nukiliya.
Haka kuma, ya zargi Iran da murƙushe masu zanga-zanga, yana mai cewa hakan na iya jawo mata tsauraran matakai daga Amurka.
[ad_2]
Source link