An dakatar da ma’aikatan lafiya 3 kan mance almakashi a cikin mara lafiya

[ad_1]



Hukumar Kula da Asibitocin ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa mutuwar Aishatu Umar ta faru ne sakamakon sakacin likitoci a Asibitin Abubakar Imam da suka mance almakashi cikinta.

A cikin sanarwar da aka fitar ranar Laraba, wacce Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Hukumar, Samira Suleiman, ta sanya wa hannu, Hukumar ta ce binciken farko da Shugaban hukumar, Dr. Mansur Mudi Nagoda, ya ba da umarnin yi ya tabbatar da cewa an bar almakashi a cikin marar lafiya bayan tiyata, wanda ya jawo mutuwarta.

Hukumar ta bayyana cewa ta dakatar da ma’aikata uku da abin ya shafa daga ayyukan asibiti nan take.

Haka kuma ta mika batun ga Kwamitin Ladabtarwa na Aikin Likitanci na Jihar Kano domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da ƙa’idojin aiki da doka.

“Hukumar tana mika ta’aziyya ta musamman ga iyalan marigayiya Aishatu Umar tare da jajantawa bisa wannan rashi mai raɗaɗi. Muna tabbatar wa jama’a cewa ba za mu taɓa lamuntar sakaci ba,” in ji sanarwar.

Aminiya ta rawaito yadda Aishatu Umar ta rasu bayan likitoci sun bar almakashi a cikinta bayan tiyata a asibitin gwamnati na Urology Centre da ke Kano.

Mijinta, Abubakar Muhammad, ya bayyana cewa matarsa ta sha fama da ciwo mai tsanani bayan tiyatar, lamarin da ya kai ga mutuwarta duk da korafe-korafen da aka yi wa asibitin.

Lamarin ya tayar da hankula a tsakanin jama’a tare da haifar da damuwa kan yadda ma’aikatan lafiya ke gudanar da aiki da kuma rashin ingantaccen tsari na ladabtarwa a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati.

Haka kuma, ’yan Najeriya da dama, musamman a kafafen sada zumunta wajen neman adalci ga marigayiya da kuma kira ga sauye-sauye a tsarin kiwon lafiya na ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *