Za a haifi jarirai 700,000 a Kano bana

[ad_1]



Gwamnatin Kano ta ƙiyasta samun haihuwar jarirai tsakanin 600,000 zuwa 700,000 a shekarar 2026, lamarin da ta ce ka iya ƙara matsin lamba ga ɓangaren kiwon lafiyar jihar.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana hakan a ƙarshen mako yayin bikin yaye ɗalibai na farko na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Sardauna da aka gudanar a Kano.

A cewarsa, an yi wannan ƙiyasi ne bisa ƙididdigar ƙaruwar yawan jama’a daga ƙidayar ’yan ƙasa da aka gudanar tun a 2006, wadda ta nuna cewa yawan al’ummar Kano na ƙaruwa da kusan kashi 3.5 cikin ɗari a duk shekara.

Dakta Nagoda ya ce wannan ƙaruwar jama’a na ci gaba da zarce adadin ma’aikatan lafiya da kayayyakin more rayuwa da ake da su, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya tsananta matsalolin da asibitocin gwamnati ke fuskanta.

Ya bayyana cewa a halin yanzu, Kano na fama da ƙarancin kusan ƙwararrun ma’aikatan lafiya 4,000, kuma yawaitar haihuwar da ake sa ran samu na iya ƙara faɗaɗa wannan giɓi tare da shafar ingancin ayyukan jinya da kula da marasa lafiya.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya nan ba da jimawa ba, tare da mayar da hankali wajen tura su zuwa yankunan da ke da ƙarancin samun kulawar lafiya, ciki har da ƙananan hukumomin Doguwa, Rogo da Sumaila.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *