Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

[ad_1]


Mai Ba da Shawara na Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan harkokin rashin fahimtar juna, Daniel Bwala, ya ce shugaba Tinubu da Shugaban Amurka Donald Trump za su gana “a cikin kwanaki masu zuwa” don tattauna zargin ikirarin kisan gillar Kiristoci a Nijeriya kwanan nan, wanda hakan ya haifar da barazanar da Shugaban Amurka ke yi wa Nijeriya.

Bwala, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce shugabannin biyu sun yi “alƙawarin” yaki da ta’addanci da tayar da zaune tsaye, ya kara da cewa, tattaunawar shugabannin za ta warware zare da abawa kan damuwar da Trump ya nuna game da zargin cin zarafin Kiristoci a Nijeriya.

In ba a manta ba, Trump kwanan nan ya zargi gwamnatin Nijeriya da yin sakaci ga hare-haren da ake kai wa Kiristoci kuma ya yi barazanar dakatar da tallafin Amurka ga Nijeriya da kuma yiwuwar kaddamar da matakin soja don “kawar da” ‘yan ta’adda da ke da alhakin kisan.

Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.

“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *