Wakilin Sin Ya Gana Da Manema Labarai Bayan Tattaunawar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakanin Tawagogin Sin Da Amurka
[ad_1]
Wakilin tattauna harkokin cinikayya na kasar Sin Li Chenggang, ya gana da manema labarai bayan tattaunawar da aka yi game da tattalin arziki da ciniki tsakanin tawagogin Sin da Amurka a birnin Paris. Inda ya ce tawagogin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi, ta hakika kuma mai ma’ana.
Ya ce Sin da Amurka sun tattauna game da samar da wani tsarin aiki a tsakaninsu, domin inganta hadin gwiwar ciniki da zuba jari, kuma sun amince cewa kyakkyawar dangantakar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu, za ta amfani kasashen biyu da ma duniya.
Ya nanata cewa, matsayar kasar Sin kan bincike na Sashe 301, ba ta taba sauya ba, kuma kasar na adawa da irin wannan bincike daga bangare guda. (FMM)
[ad_2]
Source link